Tsaron makarantu: Ribadu ya gana da shugabar UBEC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sakatariyar Zartarwa ta Hukumar Kula da Ilimin Bai ɗaya ta ƙasa (UBEC), Hajiya Aisha Garba, ta gana da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, inda suka tattauna akan wasu tsare-tsare na inganta harkar ilimi da tsaron makarantu a ƙasar nan.

Wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na UBEC Daɓid Apeh ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, ya ce ganawar ta mayar da hankali ne kan dabarun tunkarar ƙalubale a fannin ilimi.

Apeh ya ruwaito Aisha Garba tana cewa, taron na da nufin magance rashin tsaro a makarantu musamman a yankunan da ke fama da rauni da kuma samar ingantaccen ilimi ga dukkan yara.

A cewarta, taron ya bayyana muhimmiyar alaƙar da ke tsakanin ilimi da tsaron ƙasa da kuma buƙatar haɗin gwiwa tsakanin UBEC da ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro.

Wannan, inji ta, an yi shi ne domin inganta hanyoyin samun ilimi na asali da kuma tsaron makarantu a faɗin ƙasar nan.

“Wannan haɗin gwiwar yana jaddada ƙudurin gwamnati na samar da ingantaccen yanayi na ilmantarwa a matsayin wani ɓangare na babban ajandarta don ƙarfafa tsarin ilimi na ƙasa,” inji ta.

Shugaban na UBEC ya yi alƙawarin haɗa kan masu ruwa da tsaki don wargaza shingayen ilimi da samar da damar koyo ga yara a yankuna shida na ƙasar nan.

“Tare, za mu yi aiki don ƙara samun dama, inganta inganci, samar da ingantattun muhallin koyo, da samar da isassun kayan koyarwa da koyo,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, hukumar ta ƙuduri aniyar ɗaukar manufar ‘mafi dacewa’ wajen tunkarar ƙalubalen ilimi na musamman a faɗin ƙasar nan.

By ukarofi