Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a halin yanzu ba ta da wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki a ƙasar.
Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a daidai lokacin da yake cika kwanaki 100 da karɓar ragamar muƙamin.
Tegbe ya ce ya samu kiraye-kirayen waya da dama a ƙarshen mako bayan yaɗuwar rahotannin cewa Gwamnatin Tarayya na shirin ƙara kuɗin wutar lantarki.
Ya ce rahotannin ba su da tushe, inda ya bayyana cewa abin da gwamnatin ta mayar da hankali a kai shi ne inganta samar da lantarki da kuma rage matsalolin da ke addabar ɓangaren.
Ministan ya ce gwamnatin na kuma gudanar da cikakken bincike kan tsarin samar da lantarki a faɗin ƙasar domin gano matsalolin da ke akwai da kuma magance su.
Ya ƙara da cewa gwamnati na neman hanyoyin samar da makamashi masu ɗorewa, tare da inganta tsarin watsawa da rarraba lantarki.
A cewarsa, samar da ƙarin lantarki kaɗai ba zai magance matsalolin ɓangaren ba, saboda akwai matsaloli a dukkan sassan tsarin, tun daga samar da iskar gas zuwa tashoshin wutar lantarki, watsawa da rarrabawa.
Tegbe ya ce samar da lantarki da rarrabawa sun haura megawatt 5,000 a makonnin baya-bayan nan, inda mafi ƙololuwa ya kasance megawatt 5,330 a watan Agusta da Satumba.
Ya kuma bayyana cewa an mayar da tashar samar da wutar lantarki ta Alaoji mai ƙarfin megawatt 375 cikin tsarin lantarki na ƙasa bayan shafe shekaru uku ba ta aiki.
Ministan ya ce an kuma girke sabbin na’urorin canza wuta a wasu tashoshin Legas da Abuja, yayin da aka shigar da kusan mitoci 350,000 cikin kwanaki 100 na farko da ya yi a kan muƙamin.
