Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jami’ar Calabar (UNICAL) ta dakatar da wasu ɗalibai tara bisa zargin aikata satar jarrabawa da kuma wasu munanan ɗabi’u da ake zargin sun aikata tare da yaɗa su ga sauran ɗaliban jami’ar.
Hukumar gudanarwar jami’ar ce ta yanke hukuncin dakatar da ɗaliban bayan wani zama da ta gudanar, sakamakon rahoton da Sashen Kula da Munanan ɗabi’u da Satar Jarrabawa na jami’ar (SEMC) ya gabatar.
A cewar bayanan da aka samu, an ɗauki matakin ne bayan wani kwamiti da ke binciken lamarin ya gana da hukumar gudanarwar jami’ar.
Daga bisani, Magatakardar Jami’ar, Dokta Chikwuka Icha, ta sanya hannu kan takardar amincewa da dakatar da ɗaliban.
Takardar ta bayyana cewa an dakatar da ɗaliban ne daga shekarar karatu ta 2026/2027, kuma za su koma jami’ar a zangon karatu na 2027/2028 domin ci gaba da karatunsu.
ɗaliban da aka dakatar sun haɗa da waɗanda ke karatu a tsangayar koyar da harkokin nishaɗi da aikin jarida.
Hukumar jami’ar ta umarci mukaddashin shugaban Sashen Kula da Harkokin ɗalibai da shugabannin sassan da ɗaliban ke karatu da su tabbatar da sanya ido, domin ɗaliban da aka dakatar su ƙaurace wa shiga harabar jami’ar da halartar darussa a lokacin da dakatarwar ke aiki.
