Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙungiyar Izala ta ƙasa reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa ya musanya raɗe-raɗin da ake cewa Gwamnatin Tarayya ta ba ƙungiyar shinkafa buhu 6000.
A hira da ya yi da manema labarai a gidansa da ke Katsina Sheikh Yakubu Musa ya ce a saninsa Majalisar ƙoli na tabbatar da shari’a aka wannan shinkafa ta raba.
Ya cigaba da cewa, Majalisar sai ta kafa kwamitin mutum uku da ba su alhakin raba ganin ƙungiyoyi irin na ita izala da ɗariƙa da sauransu suna ƙaraashin ita majalisar ce.
Sheikh Yakubu Musa ya ƙara da cewa, kamar yadda ya sami bayani kwamitin sun raba shinkafar ba ta hannun ƙungiyoyin ba kuma sun bi ko ina suka saɓa wa malamai dauransu.
“Misali ba a bani buhu ko ɗayaba kamar yada akai ta yaɗawa wasu cewa suke na karkatar da shinkafa, “ya ce.
Ga masu wannan ƙazafi kuwa, Sheikh Yakubu Musa ya ce ya bar su da Allah.
Shugaban ƙungiyar wanda har ila yau yana ɗaya daga cikin shugabannin na kasa ya jawo hankalin shugaban ƙasa Bila Tinubu da ya sake salon shugabancin sa.
Ya ce matsalar da ake samu a gwamnatin Tunubu shine na kusa da shi basu fada masa gaskiyar halin da yan kasan ke ciki.
“Sau tarin yawa tallafi da gwamnatin tarayya ke badawa a rabawa talakawa basa zuwa gare su,sai dai karkatar da su wajan yan siyasa” Sheikh Yakubu Musa ya ce.
Sai ya yi kira ga ’yan siyasa masu riƙe da madafun iko da su ji tsoron Allah.
