Kwanaki 100 a kan karagar mulki: Yadda Farfesa Sa’adatu Liman ta inganta harkokin ilimi a NSUK

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Idan a manta ba a kwanakin baya ne jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito labarin naɗin mace ta farko a muƙamin shugabar Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa da ake fi sani da NSUK a Turance da ke birnin Keffi, hedikwatar ƙaramar Hukumar Keffi a jihar wato Farfesa Sa’adatu Hassan Liman.

A hanzu haka sabuwar shugabar ta babbar jami’ar gwamnatin jihar ta Nasarawa Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta cika kwanaki 100 a wannan karagar mulkin jami’ar.

A kan haka ne ma ya sa wakilinmu a jihar JOHN D. WADA ya gudanar da wani bincike na musamman don gano yanayin kamun ludayin nata wato ire-iren shirye-shirye da sabbin tsare-tsare da kawo yanzu cikin waɗannan kwanaki 100 da ta yi, sannan ko tsare-tsaren suna haifar da ɗa mai ido.

Don gano hakan wakilin namu ya kai wani ziyara ta musamman zuwa jami’ar ranar Litinin 5 ga watan Yulin shekarar 2024 da ake ciki inda ya samu damar gana da shugabannin shashin karatu dabandaban na jami’ar da ake kira Deans of Faculties a turance da mataimakan sabuwar shugabar jami’ar a fannonin karatu dabandaban da sauran su inda ba shakka duk suka yi amfani da damar suka yaba wa shugabar nasu Farfesa Sa’adatu Hassan Liman musamman dangane da sabbin tsare-tsare da shirye-shirye da a cikin kwanaki ɗari kacal an samu inganci da cigaba masu ma’ana da dama a duka fannonin karatun jami’ar dama yanayin gudanar da sauran harkokin jami’ar baki daya.

Waɗannan shugabannin sassan karatun jami’ar da dama da haka zanta dasu a yayin binciken na musamman sun hada dana fannin karatu na gaba da na karatun aikin jarida da na ilimin kwamfuta da na aikin jinya da na muhalli da na ilimi dana ma’adanai dana tattalin arziki da na shugabanci da na aikin noma da dai sauran su da dama inda duk suka bayyana cewa ba shakka cikin lokacin kalilan wato kwanaki 100 da sabuwar shugabar jami’ar farfesa Sa’adatu Hassan Liman tayi akan kujerar ta cimma nasarori da dama wa jami’ar fiye ma da mitsali.

Sun ce, fara aiki a matsayin sabuwar shugabar jami’ar ke da wuya sai ta fara ƙirƙiro tare da aiwatar da wasu kyawawa da muhimman ƙudurori da suke cigaba da kawo canje-canje masu ma’ana a yanzu haka wa jami’ar.

Sunce tabbas gwamnan jihar ta Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule bai yi zabin duhun dare ba na nada farfesa Sa’adatu Hassan Liman mukamin kasancewar ta tamkar mai ceto wa jami’ar da fannin ilimin jihar baki ɗaya ce.

A cewar su, farfesa Sa’adatu Hassan Liman a cikin kwanaki darin ta iya cimma burin jami’ar ne ta tattaunawa akai-akai da sauran shugabanni da ma’aikatan jami’ar baki daya inda akarshe bayan ta gano kalubalan da kowanna fannin ke fuskanta sai nan take ta fara ƙirƙiro tareda aiwatar da wasu kyawawan tsare-tsaren mafita tare da goyon bayan duka sauran shugabannin a duka matakai shiyasa acewar su basa mamakin nasarorin da ta iya cimma a cikin kwanakin 100 kacal na shugabancin ta ɗin.

Hari ila yau, waɗannan shugabannin fannonin karatun jami’ar daban-daban wato Deans of Faculties a turance waɗanda wakilin namu ya tattauna da su a lokacin binciken na musamman don gano rawar da sabuwar shugabar jami’ar ta gwamnatin jihar Nasarawa farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta taka cikin kwanaki darin sun kuma bayyana cewa bayan waɗannan nasarorin da aka samu a jami’ar gwamnatin jihar kawo yanzu cikin kwanaki 100 na shugabancin Farfesar, Sa’adatu takan kuma jagoranci sauran shugabanni da ma’aikata da malaman jami’ar akai-akai inda sukan kai ziyara na musamman yankunan jihar baki ɗaya dama wajen jihar don neman haɗin kai da sauran hukumomi da suka dace musamman a fannin ilimi baki ɗaya don tabbatar da bunƙasar harkokin ilimi a jami’ar bakiɗaya.

Sun ƙara da cewa, bayan waɗannan tsare-tsare Farfesa Sa’adatu Hassan Liman tana kuma tabbatar da horo da aiki tuƙuru tare da biyayya tsakanin malamai da ɗaliban jami’ar baki ɗaya akoyaushe musamman batun cin zarafin ɗalibai ma da yin lalata da su da wasu miyagun malamai ke yi a da a yanzu haka sannu a hankali mummunar lamarin yana zame tarihi a jami’ar da kewayen ta baki ɗaya.

Haka kuma a fannin tsaron rayuka da dukiyoyin ɗalibai da sauran malamai da ma’aikatan jami’ar baki ɗaya kawo yanzu cikin kwanaki ɗari, a cewarsu shugabar Farfesa Sa’datu dole ne a daga mata tuta a fannin kasancewar tunda da hau karagar mulkin tana aiki ne ba dare ba rana don tabbatar da tsaron jami’ar baki ɗaya musamman idan aka yi la’akari da yadda akoyaushe takan haɗa kai da sauran hukumomin tsaro da ke karamar hukumar ta Keffi inda jami’ar take da suka haɗa da rundunar ‘yan sanda da masu kare fararen hula wato Ciɓil Defence a turance da sojoji da ‘yan banga da sauran su don tabbatar ana gudanar da sintiri na musamman akai-akai a jami’ar don dakile ayyukan ‘yan ɓata-gari da sauran su.

Suma a nasu ɓangaren wasu ɗaliban jami’ar da wakilin namu ya kuma gana da su dangane da yadda za su kwatanta tsarin shugabancin sabuwar shugabar ta su, sai duk suka bayyana cewa ba shakka a yanzu kan babu abin da za su ce sai dai sambarka, don kuwa a cikin kwanaki 100 da Farfesar ta su ta yi a mulkin jami’ar ta iya magance musu wasu manya kuma mahimman matsaloli da dama da suka yi ta fuskanta a jami’ar da kewayenta baki ɗaya a kwanakin baya wato musamman na rashin ruwan sha da wutar lantarki da uwa uba tsaron lafiyar su da dukiyoyin su akoyaushe da hakan ba shakka ya sa a yanzu suke barci da idanuwan su biyu a rufe.

A cewarsu, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta magance musu matsalolin ne jim kaɗan da hawarta kujerar inda ta gayyato hukumomin daban-daban na gwamnati da ke kula fannin samar da ruwa da fannin wutan lantarkin da dai sauran su inda bayan ta gana da su bada deɗewa ba sai suka fara samun waɗannan buƙatun su a wadattace.

Haka kuma batun wuraran kwanciyar su wato Hostels a turance duk acewar ɗaliban farfesar da zuwarta cikin kwanaki ɗarin ta kammala gyare-gyaren gine-ginen da gina sabbi da samar da kariya da tsapta a wararen da sauran su musamman a fannin mata wato inda mata ɗaliban ke kwanciya ta tabbatar ta inganta yanayin wajen kasancewa itama mace ce da sauran su.

A kan haka nema yasa sai duka ɗaliban jami’ar ta jihar Nasarawa da aka zanta da su duk suka kuma yi amfani da damar inda suka yaba wa sabuwar shugabar nasu wato Farfesa Sa’adatu Hassan Liman dangane da wadannan nasarori da ta cimma a cikin kwanaki ɗarin kacal suka kuma taya ta murnar bikin cika kwanakin tare da yi mata addu’oi na musamman da fatan alheri.

Wakilinmu dai bayan wannan tattaunawa na musamman da ya yi da waɗannan rukunin ma’aikata da malamai da shugabanni da kuma ɗaliban jami’ar da sauran su ya kuma gano a yayin ziyarar binciken na musamman cewa a yanzu haka cikin kwanaki 100 na shugabar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman a kan mulkin ta kuma aiwatar da wasu mahimman gine-gine wa jami’ar da suka hada da wani babbar hotel na jami’ar da babban ɗakin drama wato wasar ƙwaiƙwayo da samar da sabbin nahurorin karatu irin na zamani wa duka fannonin karatun jami’ar daban-daban don inganta tare da bunƙasar yanayin karatu a jami’ar da tabbatar da kyakkyawar zamantakewa tsakanin malamai da ɗaliban jami’ar bakiɗaya da uwa uba riƙon amana da tabbatar da gaskiya a shugabancin jami’ar da dai sauran su inda hakan ya sa malaman da ɗaliban da duka sauran al’ummar jami’ar da garin Keffi dama jihar baki ɗaya a yanzu haka suke ta aiko da saƙonnin taya murnar su wa ita shugabar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman don taya ta murnar bukukuwan cikan ta kwanaki ɗarin a mulki.

A ƙarshe, binciken wakilinmu ya kuma gano ita dai sabuwar shugabar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman kafin wannan naɗin nata a matsayin mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar babbar jami’ar ta gwamnatin jihar Nasarawa ta kasance babbar malama ce da mataimakiyar shugaban jami’ar na da da daɗewa kuma ta yi karatu ne a fannin ilimin addinin Musulunci kuma ta ƙware sosai a fannin da hakan nema yasa wasu na ganin ana samun adalci da riƙon amana a yanzu haka a ƙarƙashin shugabancin ta a jami’ar ne a matsayin na ainihin Musulma da ke cike da tsoron Allah a harkokin ta kuma kowa ya san da hakan a jami’ar dama jihar ta Nasarawa baki ɗaya.

By ukarofi