Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hannun Ministan Ayyuka, David Umahi, ta miƙa tuhuma ga ɗan kwangilar da ya yi aikin titin Maiduguri-Kano a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, titin da ya lalace sakamakon ambaliyar ruwa a kwanan nan.
Titin ya kasance sashe na uku na sabon titin Kano-Maiduguri da aka gyara ba da jimawa ba.
A cikin wata sanarwa daga mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Orji Uchenna Orji, Umahi ya bayyana cewa, abin takaici ne ganin yadda hanyoyin da aka kammala a ƙasar ba su kai wa tsawon shekara biyar.
Umahi ya ce, an tura wata tawaga daga ma’aikatar don duba irin ɓarnar da ruwan ya yi, kuma ya yi alƙawarin samun mafita mai ɗorewa ga wannan hanya.
Ya kuma sanar da dakatar da sashe na ɗaya na titin Kano-Maiduguri da aka ba wa Kamfanin Ɗantata & Sawoe Ltd tun daga shekarar 2007, saboda wuce wa’adin lokacin kammala shi.
“Ina umartar Daraktan Kula da Gyara Manyan Hanyoyi da ya haɗa kai da Babban Sakataren na Ma’aikatar Ayyuka, domin a tura wasu mutanen zuwa can don su ga abin da za mu iya yi a wurin, kuma abin takaici ne cewa idan aka kammala aiki da kwangila, ba ma jin daɗin hanyoyin na tsawon shekaru biyar.”
Yayin da yake magana a wajen taron bita kan ayyukan da aka gudanar tare da kamfanin Ɗangote, kamfani BUA da kamfanin Mainstream Energy a kan ayyukan hanyoyin da ake yi a ƙarƙashin tsarin tara haraji don zuba hannun jari a fannin manyan ayyuka, ‘Road Infrastructure Development and Refurbishment Investment Tax Credit Scheme’.
Ya ce, daga yanzu za a sami yarjejeniya kan kammala ayyukan da ake yi da kuma jaddawalin lokacin kammala ayyukan daban-daban da ake yi a ƙarƙashin tsarin harajin.
