
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
An tilasta wa jirgin tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump sauka a yankin Billings da ke jihar Montana bayan da ya samu tseko akan hanyarsa ta zuwa Bozeman.
Jami’an filin jiragen sama suka shaidawa tashar CBS aukuwar lamarin a ranar Juma’a.
Trump zai ƙaddamar da wani gangamin siyasa ne a Bozeman da ke jihar wanda hakan bai yiwuwa ba saboda tasgaro da aka samu wanda ya sanya ya sauka a Billings mai nisan mil 150 tsakanin sa da asalin inda aka shirya taron.
Baya ga haka ne, Trump ya tafi Bozeman a wani jirginsa mai tashin angulu.
Kawo yanzu dai ba a samu bayanin haƙiƙanin abin da ya sami jirgin nasa ba.
