“Na ɗauki Alan Waƙa a matsayin ɗan’uwana”
(Ci gaba daga makon jiya)
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Sunan Fatima Abba Gana ba ɓoyayye ba ne a tsakanin marubutan adabi na Nijeriya, musamman saboda yadda take da zumunci da ilimin zama da jama’a. Bayan kasancewarta marubuciya, Fatima ta kasance tsohuwar ma’aikaciyar banki, ýar kasuwa, kuma ƙwararriya kan binciken shigi-da-ficen kuɗi. Ta rubuta littattafai daban-daban cikin harshen Hausa da Turanci, inda take mayar da hankali kan labaran da suka shafi raya al’ada, inda zamantakewa da kyautata tarbiyya. Ita ce ta rubuta littafi mafi girma da wata marubuciya a Arewa ta wallafa, domin kuwa littafin ta na Bunayya an raba shi har kashi huɗu kuma kowanne ɓangare na ɗauke ne da labari mai kama zuciya da riƙe mai karatu. Fatima Abba Gana, mamba ce a ƙungiyoyin marubuta daban-daban na duniya.
MANHAJA: Yaya ki ke fuskantar ƙalubalen kasuwancin littattafanki? Kina mayar da kuɗinki kuwa?
FATIMA GANA: Gaskiya bana fuskantar wani ƙalubale a kasuwancin sayar da littattafaina ta kowanne ɓangare. Alhamdulillah, a gaskiya ba laifi ana mayarwa.
Kin taɓa tunanin buɗe shafi a manhajar YouTube domin karanta littattafanki zuwa murya, kamar yadda wasu marubuta ke yi?
E, a gaskiya ina da shafi a manhajar YouTube, amma ba don karanta littattafaina na buɗe su ba, domin kamfanina na buɗe, domin idan aka fara karantawa a wannan manhajar to, za a samu giɓi a kasuwancin sayar da littattafaina. Amma akwai wasu daga cikin littattafaina da aka sa a manhajar Amazon yanzu haka.
Yaya ki ke ganin tasirin fasahar sadarwa ta zamani wajen tallata littattafanki?
Gaskiya ina ganin tasirin fasahar zamani wajen tallata littattafaina, domin mafi yawan lokaci idan mutane suna son littattafaina a ƙasar waje ta wannan kafofin suke min magana, kuma a aika masu har ƙasar da suke. Saboda haka na gamsu fasahar zamani tana tasiri sosai a gareni. Kuma nakan yi amfani da zaurukan sada zumunta wajen tallata sabbin littattafaina. Sannan ina da masu taimaka min wajen dillancin littattafaina, a yawancin garuruwan Arewacin Nijeriya har da Legas, akwai kuma a shagunan sayar da littattafai. Hakan yana ƙara samar wa da littattafan inganci da daraja. Kasancewata mamba a wata babbar ƙungiyar marubuta ta Amurka, (IWW), wacce yawancin littattafan membobinta ana tallata su ne a mujallar ƙungiya da kafofin ƙungiya manya-manya, shi ne ya sa ma wasu littattafaina suke fara fita a can kafin a buga a nan gida Nijeriya. Gaskiya ta wannan ɓangaren, Alhamdullahi.
Mene ne dangantakar ki da Sarkin Adabin ƙasar Hausa, Alhaji Aminu Ladan Abubakar, wanda har ya waƙe ki da littattafanki, wanda ba kasafai ake samun haka daga marubuta ba?
Dangantaka ta da Sarkin Adabin ƙasar Hausa Alhaji Aminu Ladan Abubakar da kuma dalilin da ya sa ya wake ni da littattafaina wanda gaskiya kowa ya sani ba kasafai ake samun haka daga marubuta ba, kamar yadda ka ce shi ne na farko. Ni dai na kasance tsohuwar masoyiyar sauraron waƙoƙinsa ne, don babu waƙar da zai yi da bani da ita ko na san ta ba. Kuma a tsawon shekaru sama da ashirin na san shi, lokacin da nake aiki a banki, inda ya kan zo Kaduna wasa, ni kuma na kan je in gan wasan sa. Don haka alaƙar mu da shi ta daɗe sosai, muna zumunci da shi sosai.
Ala aminina ne, yayana ne, kuma abokin shawarata ne. Na ɗauke shi a matsayin ɗan’uwana kuma mutumin da ya san ya kamata. Yana da sanin darajar mutane da kuma mutunci, riƙon amana da faɗin gaskiya. Lokacin da na yi taron ƙaddamar da littattafaina guda biyu a Kaduna, Raƙiba da Karima. Yana ɗaya daga cikin waɗanda suke masu shirye-shiryen taron nima kaina lokacin gaskiya ban sani ba, ashe zai yi min waƙar ta musamman ta littattafaina.
Wannan halarci da ya nuna min ya ƙara ƙarfin kusancin mu da zumuncin da ke tsakanin ya kuma burge baƙin da suka je wannan taron. Ni kaina na ji daɗi sosai, wannan waƙar ta rufe min ƙofa da tunanina, domin yaba ni mamaki, kuma kowa ya sani shi ba kuɗin ka ko wani abu zai saka shi ya yi maka waƙa ba, sai dai ganin cancanta. Lokacin da na ji waƙar da yake yi fashewa na yi da kukan murnar farin ciki, ya ƙarawa taron armashi sosai. Har abada ba zan daina godiya da yi masa addu’ar fatan alheri ba. Allah Ya ƙara girma da ɗaukaka.
Kin kasance ýar kasuwa, tsohuwar ma’aikaciyar banki, da sauran harkoki na cigaban rayuwa. Yaya ki ke iya haɗa waɗannan abubuwa daban-daban, da harkar rubuce-rubuce?
Kowacce harka na sa gaba tana da lokacinta, lokacin da nake rubutu ba ya shiga hurumin ayyukan ofis, da kuma kasuwancin da nake yi, da kuma na kamfanina da kuma kula da al’umma da fassarar ayyuka idan aka bani. Domin ko lokacin da nake banki kafin in yi ritaya da safe zuwa dare ni ma’akaciyar banki ce, da tsakar dare kuma ina marubuciya ko manazarciya. Haka nake raba lokacina, bana bari wani ya shiga cikin lokacin wani.
Wanne lokaci ne ya fi miki daɗi yayin da ki ke son yin rubutu ko karatu?
Gaskiya na fi son yanayin lokacin da dare ya riga ya tsala kamar daga ƙarfe ɗaya zuwa irin bayan la’asar liƙis, a lokacin na fi jin daɗin rubuce-rubucena. Kuma aikina ya kan tafi daidai wadaida, ba tare da wani abu ya dame ni ba ko hayaniya. Sannan lokacin damina kuma nakan so in yi rubutu wajen kusa da ruwa daga wajen ƙarfe uku zuwa yamma likis shi ma ina so in yi rubutu a wannan lokacin.
Idan kina son samun natsuwa da kaucewa hayaniya me ki ka fi yi?
Idan ina son nutsuwa da kaucewa hayaniya na fi son in keɓe ni kaɗai inda ba kowa, in kwanta in ɗauko ɗaya daga cikin littattafaina, in karanta ko in yi gyaran aikin rubutun da nake yi, ko wani aikin fassara da aka bani in yi.
Yaya alaƙarki take da sauran marubuta?
Gaskiya ina da kyakkyawar alaƙa da sauran marubuta ‘yan’uwana maza da mata, bani da matsala da su.
Mene ne burinki nan gaba a harkar rubutun adabi?
Burina a gaba a harkan rubutun adabi shi ne littattafaina su karaɗe duniya bakiɗaya, duniya ta sanni a matsayina na fitacciyar marubuciya in kuma taka irin sawun su Farfesa Wole Soyinka, in samu babban kambun da ake karrama marubuta na duniya da shi, wato in zama Nobel Laureate.
Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?
Mutum mugun icce.
