Ba ni da hannu a yunƙurin kashe Wike – Danagogo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon ministan wasanni a Nijeriya, Dakta Tammy Danagogo, ya musanta zargin da ake yi cewa yana da hannu a wani yunƙurin kashe ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Fatakwal da yammacin ranar Litinin, tsohon Ministan wasannin ya yi watsi da zarge-zargen da aka yi masa, inda ya ce ba su da tushe balle makama.

Sanarwar wadda mataimakinsa na musamman, Barista Obele Briggs ya sanya wa hannu, ta ce Danagogo bai taɓa shiga wata tattaunawa, ko taro ko shiri da ya shafi kitsa tashin hankali, ko kuma wani aiki da ya saɓa wa dokar Nijeriya ba.

A ɗaya gefe, rahotannin sun ce jami’an tsaro na sashen leƙen asiri daga ofishin babban Sufeton ‘yan sandan Nijeriya sun kama wani likita kuma fasto da ke birnin Fatakwal na jihar Ribas, mai suna Tombari Gbeneol, bisa zarginsa shi ma da kitsa yadda za a hallaka ministan.

Rahotanni sun ce kamen ya biyo bayan gano wata tattaunawa ta wayar tarho da ake zargin an yi tsakanin Fasto Gbeneol da Danagogo, wanda shi ne tsohon sakataren gwamnatin jihar Ribas.

A cikin tattaunawar da aka ce an naɗa, ana zargin sun tattauna shirin shigo da wasu ‘yan Isra’ila domin aiwatar da kisan ministan babban birnin tarayyar.

Rahoton ya ƙara da cewa an kammala tattaunawar da zargin shirin neman kuɗin aiwatar da kisan, daga hannun gwamnan jihar Ribad, Siminalayi Fubara.

Sai dai, dakta Danagogo ya ƙi amincewa da zarge-zargen baki-ɗaya, yana mai cewa ƙarya ce tsagwaronta kuma an ƙirƙire ta domin ɓata masa suna.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan rahotanni da ya bayyana a matsayin ƙarya kuma masu tayar da hankali.

By ukarofi