Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Litinin gwamnatin Nijeriya ta sanar ɗaukar sabbin matakai na magance matsalar satar jarrabawa a yayin rubuta jarrabawar kammala makarantar sakandare (SSCE).
Akwai hukumomi da ke shirya jarrabawa da suka haɗa da: WAEC da NECO da NABTEB da sauransu. Kuma wajibi duk mai neman gurbin karatu a manyan makarantu ya gabatar da shaidar samun nasarar a ɗaya daga ciki ko biyu daga cikin waɗanna jarrabawowi.
A cikin jawabin mai magana da yawun ma’aikatar ilimi, Folasade Boriowo, ya fitar, ya ce, gwamnati ta sanar da ɗaukar matakai da nufin kyautata sahihancin jarrabawar da dawo da ƙarfin guiwar al’umma kan tsarin gudanar da jarrabawar.
A yayin da yake bayyana abin da ministan ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana cikin jawabin da ya ce, ya ce, matakan da aka ɗauka sun haɗa da ɓullo da tsarin tarwatsa jerin yadda aka rubuta tambayoyin.
“Duk da cewa ɗalibai za su amsa dukkan tambayoyi iri ɗaya, amma za a tarwatsa lambobin tambayoyin ta yadda na kowanne ɗalibi zai bambanta da na ɗan uwansa. Wannan zai sa kowanne ɗalibi ya rubuta jarrabawa da ta ƙeɓanta gare shi wanda zai rage damar satar amsa,” in ji jawabin.
Gwamnati ta ce ta ɓullo da sabbin hanyoyin tattara maki na makaranta da aka fi sani da “Continuous Assessment (CA)” wanda lallai ne hukumomin shirya jarrabawar su yi amfani da shi.
A cewar jawabin, makin cike gurbin na 1 (CA), za a tura shi ne a watan Janairu a yayin da za a tura makin cike gurbi na 2 a watan Afirilu, sai kuma makin cike gurbin na 3 a watan Agusta.
“Waɗannan matakai wajibi ne a yi amfani da su domin tabbatar da tafi da abubuwa yadda ya kamata da sahihancin bayanai wajen tafi da makin cike gurbi na ɗalibai a faɗin ƙasar nan,” sanarwar ta bayyana.
Haka kuma gwamnati ta ɓullo da tsarin rajistar ɗalibai ta hanyar samar wa kowannensu da lamba ta musamman.
Lambobin za su taimaka wajen bin diddigin ɗalibi a yayin rubuta jarrabawar “wajen tabbatar da sa-ido da taimaka wa tsarin tantance ɗalibai da ba su takardar shaidar kammala makaranta da zama hanyar kula da bayanansu.”
“Maikatar ilimin ta bai wa masu ruwa da tsaki wajen shirya jarrabawar tabbacin za ta yi aiki da dukkan hukumomin wajen sa-ido da tafi da al’amuran jarrabawar bisa tanadin doka.”
An bayyana cewa waɗannan matakai na nuna yadda gwamnatin tarayya ta himmatu wajen tabbatar da an yi sahihiyar jarrabawa mai cike da adalci da kuma bin tsarin da duniya ke kai a yayin magance matsalolin da suka daɗe suna damun ƙasar nan,” in ji jawabin.
A watan da ya gabata, gwamnati ta haramta sauya wa ɗalibai makaranta da ke aji 3 na babban makarantar sakandare.
An ɗauki matakin ne domin kawo ƙarshen tsallakawa wasu makarantu da cibiyoyi domin rubuta jarrabawa da ake zargi kan jawo satar amsa ko bai wa ɗaliban amsa a yayin rubuta jarrabawar.
