Ba za a samu layukan mai ba yayin Kirsimeti – Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa zagayowar layukan neman man fetur da kan addabi ƙasa musamman lokacin bikin Kirsimeti sun zama tarihi, domin matatarsa za ta wadatar da buƙatar ƙasa baki ɗaya.

Da yake zanta wa manema labarai a Fadar Shugaban ƙasa bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu, Dangote ya ce sun riga sun sanar da Hukumar NMDPRA cewa matatar tana da ƙarfin samar da lita milyan 50 a kullum, wanda ya zarce buƙatar cinikin cikin gida.

Ya ce, tun daga shekarar 1972 Nijeriya ke fama da layin man fetur, “amma a yau, mu ne kaɗai a tarihin ƙasar da muka kawar da layin ba ta hanyar shigo da mai ba, sai ta hanyar samarwa a gida. Ko lokacin da muke aikin gyaran sassan matatar, ba a samu layi ba. Ina tabbatar maku, layi ya zama tarihi.”

Dangote ya ƙara da cewa, makwabtan Nijeriya suma za su amfana, inda daga Fabrairu 2026 za su riƙa samar da man da ya kai lita milyan 15 zuwa 20 fiye da buƙatar ƙasar, wanda hakan ya wajabta fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.

Game da masana’antun cikin gida, ya ce sashen sarrafa robobi zai samu sauƙi, domin a baya suna kashe dala milyan 400 wajen shigo da kayan haɗa robobi, amma yanzu su ne za su mora mafi yawan riba.

Ya bayyana cewa, shirin dogon lokaci shi ne faɗaɗa masana’antar zuwa ganga milyan 1.4 a rana nan da 2028, wanda zai wuce masana’antar Reliance ta India – mafi girma a duniya a yanzu.

Haka kuma ya ce ana kan shirin kai noman urea zuwa ton milyan 12 a shekara, wanda zai kai Nijeriya gaba da Rasha da ƙatar a samar da takin zamani.

“Muna son mu zama cibiyar takin Afirka baki ɗaya,” inji shi.

Dangote ya danganta saukar farashin fetur da dizal da karuwar gasa da kuma raguwar fasa-kwauri. “Farashi na sauka ne saboda tilas mu yi gasa da shigo da mai. Abin farin ciki, fasa-kwauri ya ragu sosai, kodayake ba gaba ɗaya ba.”

Ya ce, wannan zuba jari ba don gaggawar maida kuɗin da aka kashe ba ne: “Ba mu zo nan mu dawo da dala biliyan 20 cikin dare ba. Wannan jarin dogon lokaci ne. Abin da nake son bari a matsayin tarihi shi ne: duk abin da ‘yan Nijeriya ke buƙata — mai, taki, wuta — mu kasance cikin waɗanda suka samar.”

Dangote ya jinjina wa tsarin ɗanyen mai a naira na gwamnatin Tinubu, yana kiransa “mataki na kishin ƙasa” duk da yadda wasu manyan kamfanonin mai na waje suka fara nuna adawa.

By ukarofi