Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ba za su fuskanci wani zalunci ba a aiwatar da sabon tsarin haraji da zai fara aiki daga 1 ga Janairu 2026.
Shugaban Kwamitin Aiwartar da Sabon Tsarin Haraji na ƙasa (National Taɗ Policy Implementation Committee), Joseph Tegbe, ne ya bayyana haka, yana mai cewa kwamitin ya ƙuduri aniyar aiwatar da tsarin ba tare da jawo cikas ga tattalin arzikin ƙasa ba.
An ƙaddamar da kwamitin ne a ranar Juma’a a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Kuɗi da Kodinetan Tattalin Arzikin ƙasa, Mista Wale Edun.
An naɗa Sanyade Okoli, Mashawarcin Shugaban ƙasa kan Kuɗi da Tattalin Arziki, a matsayin sakatariyar kwamitin. Wannan ƙaddamarwa na ɗauke da muhimmiyar ma’ana wajen inganta tsarin haraji domin gina tsari na zamani, ingantacce, kuma mai adalci ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.
Yayin da yake magana da ‘yan jarida bayan taron, Tegbe ya ce yana sane da fargabar da ta taso kan sabon tsarin, yana mai ba da tabbacin cewa kwamitin zai bi duk matakai na warware damuwar jama’a.
Ya ce, sabon tsarin haraji na da niyyar sassauta harkokin kasuwanci, daidaita fassarar dokokin haraji tsakanin jihohi da tarayya, tare da inganta adalci ga masu biyan haraji.
Ya ce, “Aikin da ke gabanmu babba ne, mai matuƙar muhimmanci ga cigaban ƙasa. Waɗannan dokoki za su sauya tsarin gudanar da haraji, su haɗa fassara tsakanin matakan gwamnati, su kuma tabbatar da ingantaccen yanayin kasuwanci. Muna tabbatar wa ‘yan Nijeriya da masu zuba jari cewa aiwatarwa za ta kasance mai gaskiya, tsabta, kuma mai mutunta dan adam.”
Tegbe ya ƙara da cewa, sabon tsarin zai mutunta haƙƙin masu biyan haraji, ya rage ruɗani, sannan ya kare marasa galihu daga tasirin da ka iya cutar da su.
Ya tabbatar da cewa kwamitin zai ci gaba da tattaunawa da kamfanoni, jihohi, ƙungiyoyin farar hula, da ƙungiyoyin ƙwararru domin tabbatar da cewa kowa na da hannu a tsarin.
Game da fargabar shisshigi cikin asusun bankunan jama’a, Tegbe ya musanta hakan. Ya ce, “Gwamnati ba ta da wani yanki na kutsa kai cikin asusun mutane ba tare da dalili ba. Ba a bincike ‘yan Nijeriya, ba a kuma sa su ƙarƙashin tuhuma.”
Kan rikicin Capital Gains Tax (CGT), Tegbe ya ce kwamitin na sane da ƙorafe-ƙorafen da jama’a da masana suka tashi da su.
Ya ce, “Mun fahimci damuwar da CGT ya haifar, har ma ya tayar da tarzoma a kasuwar hannayen jari, abin da ya sa Minista ya shiga tsakani. Kwanaki masu zuwa za mu sake duba wasu sassa domin gyara inda ake buƙatar gyara. Ko da yake dokar za ta fara aiki 1 ga Janairu, akwai yuwuwar a tashi da wasu sauye-sauye domin biyan buƙatar jama’a.”
