Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da faɗaɗa shirin horar da ’yan soshiyal midiya, waɗanda aka fi sani da ‘content creators’ kan sabbin dokokin haraji daga mutum 20 zuwa 50, bayan matsin lamba da suka taso daga ɓangarori daban-daban na jama’a.
Shugaban Kwamitin Sauye-sauyen Haraji da Tsare-tsaren Kuɗi na Fadar Shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya sanar da faɗaɗa shirin a ranar Lahadi, inda ya ce an bi diddigin ƙorafe-ƙorafen jama’a game da rashin daidaito a jerin waɗanda aka fara zaɓa.
A ranar Asabar ne kwamitin ya fitar da sunayen ‘yan soshiyal midiya 20 da ya bayyana a matsayin manya a fagen ƙirƙira, domin shiga shirin horon musamman kan dokokin haraji.
Kwamitin ya ce, zaɓen na farko ya samo asali ne daga ƙarin sha’awar jama’a kan bayanan da suka fi sauƙi da fahimta game da sauye-sauyen harajin da gwamnati ke aiwatarwa.
An zaɓi ‘yan soshiyal midiya ɗin ne bisa girman mabiyan da suke da su a dandamali kamar YouTube, TikTok, Instagram, Facebook da ɗ.
Sai dai jerin sunayen farko ya tayar da ƙura, inda aka yi zargin rashin daidaiton yankuna da ƙin saka ’yan soshiyal midiya daga wasu ɓangarorin ƙasar.
Wani hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya bayyana a ɗ cewa zaɓen bai nuna wakilci na ƙasa ba, musamman ganin babu ko ɗaya daga Arewa.
Ya ce, shirin wayar da kan jama’a kan haraji ya kamata ya ƙunshi ‘yan soshiyal midiya daga ko ina a ƙasar, domin saƙon ya isa ga kowa cikin yare da murya da ya saba ji.
A sakamakon matsin lambar, Taiwo Oyedele ya sanar a ranar Lahadi cewa kwamitin ya faɗaɗa shirin zuwa mutum 50, tare da buɗe ƙofa ga ƙarin masu sha’awa da suka cika sharuɗɗa.
Daga cikin sharuɗɗan akwai samun aƙalla mabiyan 10,000 gaba ɗaya a kafofin sada zumunta daban-daban, da kuma nuna ƙarfin halin halartar horo da neman ƙarin bayani domin tabbatar da ingancin bayanai kafin yaɗa su ga jama’a.
Ya ce, bayan kammala horon, mazarta za su samu damar yin tambaya kai tsaye gare shi da sauran manyan jiga-jigan kwamitin kafin su wallafa bayanai, domin tabbatar da gaskiya da inganci.
Ana sa ran fitar da sabon jerin sunayen mutum 50 bayan an kammala horon. Ana rufe karɓar nomineɗan a ranar Litinin, 8 ga Disamba, 2025.
