Hukumar CAC za ta rufe masu ‘POS’ da ba su yi rajista ba 1 ga Janairun 2025

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni ta Nijeriya (CAC) ta gargadi cewa daga 1 ga Janairu, 2026, za ta fara ɗaukar mataki mai tsauri kan duk masu gudanar da harkokin ‘Point of Sale’ (POS) da ba su yi rajista da hukumar ba, tare da bayyana cewa lokacin sassauci ya ƙare.

A cikin sanarwar da CAC ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta jaddada cewa dole ne kowanne mai POS ya tabbatar da cikar dukkan ƙa’idoji, musamman yin rajista a matsayin kamfani ko mallakar kasuwanci na mutum ɗaya, domin daidaita harkokin cinikayya da kariyar tsarin kuɗi a ƙasar.

Hukumar ta ce, daga ranar da ta ƙayyade, duk POS ɗin da bai cika sharuɗɗa ba za a rufe shi nan take, tare da sanar da hukumomin tsaro domin tabbatar da aiwatar da doka.

“Babu wani mai POS da zai ci gaba da aiki ba tare da rajista ba. Mun umarci hukumomin tsaro da su tabbatar cewa doka ta yi aiki a ko’ina cikin ƙasar,” inji sanarwar.

CAC ta yi nuni da cewa, matsalar yawaitar masu POS da ba su da rajista na kara ta’azzara matsalolin tsaro da hadarin zamba a harkokin kuɗi, musamman ganin yadda wasu kamfanonin Fintech ke taimaka wa ayyukan da suka saɓawa doka.

Sanarwar ta ce, wannan yanayi na iya jefa tsarin hada-hadar kuɗi a ruɗani, tare da barazana ga jarin ɗan ƙasa. Hakan ya sa hukumar ta ce lokaci ya yi da za a “taka wa masu take dokoki birki domin kare tsarin tattalin arziƙin da lafiyar harkokin kasuwanci.”

Ta ƙara da cewa, yin rajista bai ɗauki lokaci ba, kuma yana da matuƙar muhimmanci wajen bai wa masu POS kariya daga matsalolin shari’a, da kuma tabbatar da cewa suna aiki a bisa tsarin doka kamar sauran masu gudanar da harkokin kasuwanci.

CAC ta kuma buƙaci jama’a da su kasance masu lura wajen mu’amala da masu POS, ta yadda za su yi aiki da kamfanoni masu lasisi, domin guje wa faɗawa cikin zamba ko asarar kuɗi.

By ukarofi