Ba za mu bar ƙauyukan kakannin mu na gado saboda ambaliya ba, mazauna yankin kogi ga gwamnatin Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

An yi kira na musamman ga mazauna kusa da kogi su riƙa bin umurnin gwamnati na yin kaura daga yankunan don guje wa ambaliya da ka iya aukuwa a kowane lokaci.

Babban sakataren dindindin na ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa na gwamnatin jihar Nasarwa Honorabul Mohammed Garba Rosha ne ya yi wannan kira a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishinsa dake ma’aikatar a Lafiya babban birnin jihar a mako da ake ciki.

Ya ce kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yadda ya kasance duk da gargaɗin ƙwararru da kuma gwamnatoti a duka matakai cewa waɗanda ke zaune a yankunan manyan kogunan a jihar su yi ƙaura sakamakon ambaliya da ake ganin zai iya aukuwa a kowane lokaci sakamakon buɗe babban dam na ƙasar Kamaru amma duk da hakan sai waɗannan al’ummar suka ƙi bin umurnin.

A cewarsa kawo yanzu gwamnatin jihar ta sanar tare da wayar da kawunan waɗannan mutane dangane da illoli da hatsarin cigaba da zama a kusa da manyan kogunan amma galibi suka yi kunnen uwar shegu wa umurnin na musamman.

Babban sakataren dindindin na ma’aikatar muhallin da albarkatun ƙasa Honorabul Mohammed Garba Rosha ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar cewa ƙauyuka dake kusa da manyan kogunan a jihar da suke kuma fuskantar barazanar aukuwar ambaliyar sun haɗa da Tunga dake yankin ƙaramar Hukumar Awe a jihar da Rukubi a Doma da Udeni da Loko a ƙaramar hukumar Nasarawa da Umasha a ƙaramar hukumar Toto da sauransu.

Dangane da ko menene dalilin ƙin bin umurnin gwamnati ɗin daga mazauna yankunan sai Honorabul Mohammed Garba Rosha ya bayyana cewa galibin waɗanda abin ya shafa suna bayyana cewa ba za su iya barin yankunan ba ne don wai ƙauyukan kakaninsu ne na gado saboda haka ba za su iya barin wuraren ba inda ya ce tabbas wannan mataki ne dake tattare da babban hatsari.

Wakilinmu dai a jihar ta Nasarawa John D. Wada kawo yanzu bincikensa ya gano cewa tuni ruwan waɗannan manyan kogunan yankunan da aka ambato suna cigaba da ƙaruwa sa’anan suna kuma ci gaba da kusantar waɗannan ƙauyukan a hankali a yayin da su kuma anasu ɓangaren mazauna kauyukan ke cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba ba tare da nuna fargabar lamarin ba.

By ukarofi