Sarkin Kabin Argungu ya gargaɗi masu sayen abinci su ɓoye

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Majalisar Maimartaba Sarkin Kabin Argungu da ke jihar Kebbi ta haramta saye ko sayar da gero, shinkafa, wake da sauran nau’o’in abinci da waɗansu marasa kishin kai ke yi a gefen hanya ko a wani dandali inda su ke tariyar ‘yan mata da ke shigowa da abinci daga ƙauyuka domin kai kasuwa.

Ya yi wannan jawabi ne a fadarsa da ke garin Argungu ranar Juma’a’ar da ta gabata yayin zaman majalisar tare da kansilolin masarautar.

Basaraken ya nuna ɓacin ransa bisa ga yadda waɗannan mutanen ke hana ƙauyawa isa kasuwa don sayar da amfanin gonarsu.

Basaraken ya bayyana masu irin wannan ɗabi’ar a matsayin marasa imani da su da tausayi a cikin rayuwarsu tare da bayar da dama ga jami’an tsaro da ‘yan banga da su kama duk wanda aka gani yana irin wannan kasuwanci don gudanar da shi a gaban shari’a.

An bai wa jami’an tsaro cikakkar dama ta kama duk wani ko wata da aka ya karya wannan dokar, inji shi.

“Daga yau duk wanda zai saye ko sayar da gero, shinkafa, wake, masara da duk wani nau’o’in abinci to dole ne ya je kasuwa saboda an yi tanadin wurare na musamman don irin wannan kasuwanci, amma ba daidai ba ne a rinƙa taryar mutane a kan hanya ana saye abinci da araha a ɓoye har sai ya yi tsada sannan a fitar ana sayarwa al’umma.”

Ya ƙara da cewa an bai wa limaman masallatai musamman na Juma’a da su yaɗa wannan saƙon a cikin huɗubobinsu tare da yin nasihohi wa al’umma don sauke nauyin da ke wuyansu.  

By ukarofi