Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sanar da tsare wani matashi mai shekara 25, Chibunnma Chimelie, saboda zargin kashe mahaifinsa mai shakara 68.
Kakakin rundunar SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da faruwar al’amarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa, NAN, a ranar Juma’a a jihar Legas.
Ya ce al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 10:00 na dare a unguwar Isolo.
Kakakin ya ce ɗan uwan wanda ake zargin ne ya sanar da ofishin ‘yan sanda da ke Aswani.
ɗan uwan mai laifin ya ce shi ma wani maƙocin gidan da mahifinsu ke zaune ne ya kira shi, inda ya ce ga baban nasu da wanda ake zargin suna musayar yawu kasancewar suna zaune ne a gida ɗaya.
Daga nan ne ya ruga zuwa gida, sai dai ko da isarsa sai ya tarar da mahifin nasu kwance a cikin jini.
Kakakin ya ce jami’an ‘yan sanda ne suka yi wa gidan dirar mikiya tare da samun nasarar cafke wanda ke zargin kuma bayan isar jami’an bincike ne suka samu wata wuƙa mai yararin jin kusa da gawar.
Daga nan ne aka ɗauki hotunan wurin da abin ya faru tare da kai gawar babban asibitin Isolo inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Kuma tuni aka ajiye gawar a ɗakin ajiye gawarwaki. Kuma shi ma wanda ake zargi da wannan aika-aika, ya amsa laifinsa.
A ƙarshe kakakin ya ce rundunar na cigaba da faɗaɗa bincike kan faruwar wannan al’amari.
