Ba za mu yi watsi da burinmu na cimma nasara ba

Daga BILKISU XIN

Ita ce Shui Qingxia, mai horar da ‘yan wasan ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Sin, tun bayan kama kujerar take ɗaukar nauyi da ƙalubale na jagorantar ƙungiyar fita daga mawuyacin hali. Tana ƙoƙari tare da ƙungiyarta don mika wata takardar amsa ta cimma gasar ta kofin Asiya ga al’ummar ƙasar baki ɗaya. Da taushin hali da jajircewarta, ta canza makomar ƙungiyarta, da makomar gungun ’yan mata, har ma da nata makoma.

A shekarar 1983, Shui Qingxia mai shekarun haihuwa 17 a duniya ta samu horo kan wasan guje-guje da tsalle-tsalle a Makarantar Wasannin Matasa ta yankin Hongkou na birnin Shanghai dake gabashin ƙasar Sin. Ta yi ta haka har tsawon shekaru 6, kuma ta zama zakaran pentathlon na ɗaliban makarantar sakandare ta Shanghai. A wancan lokacin, tana fatan samun damar haskawa a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, amma an gaya mata cewa saboda tsayin da take da shi, idan ta ci gaba da yin wasan, to ba za ta samu sakamako mafi kyau ba.

Amma, abin farin ciki shi ne, kocin makarantar wasannin yana ganin cewa, Shui Qingxia na da hazaka, kuma abin takaici ne idan aka yi watsi da ita. A daidai wannan lokaci, an kafa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata a Shanghai, don haka kocin ya ba da shawarar shigar da Shui Qingxia ƙungiyar.

Lokacin da ta sami labarin cewa, za ta yi wasan ƙwallon ƙafa, Shui Qingxia ta yi mamaki sosai, ta ce, “Me ya sa aka bar ni in buga ƙwallon ƙafa? ‘Yan mata suna buga ƙwallon ƙafa, yana da ‘ban tsoro’!”

Irin abun da take ji ba abin mamaki ba ne. A wancan lokacin, wasan ƙwallon ƙafa na mata ya kasance sabon abu a birnin Shanghai har ma a ƙasar Sin baki ɗaya, don haka yawancin Sinawa ba su fahimce shi sosai ba.

Shui Qingxia

A wancan lokacin, Shui Qingxia ba ta tsammanin cewa, wasan ƙwallon ƙafa, wanda ya sa ta dan jinkirta, zai zama “babban jigo” da ba za ta iya yin ƙasa a gwiwa ba a rayuwarta ta nan gaba. A lokacin, tunaninta ya kasance mai sauƙi ƙwarai, “Tun da ana son in buga ƙwallon ƙafa, to bari in buga.”

Don haka, Shui Qingxia ta fara wasan ƙwallon ƙafa a hukumance.

Lokacin da ta fara wasan ƙwallon ƙafa, Shui Qingxia ba ta san yadda za ta kare kanta ba, kuma ta kan ji rauni. Ko da yake wasan ƙwallon ƙafa yana da wahala, amma Shui Qingxia ta yi mamakin ganin cewa, tana da hazaƙa a wannan wasan. Tare da hazaka da kuma ƙoƙarin da take yi, Shui Qingxia ta yi sauri ta fice daga ’yan matan ƙungiyar sama da 100, kuma ta shiga tawagar farko ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Shanghai a shekarar 1984. Kana, a shekarar 1986, an zaɓe ta shiga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Sin.

Shui Qingxia ta kasance mai nazarin wasan ƙwallon ƙafa a ko da yaushe, a lokacin hutu, ta kan shafe yawacin lokuta wajen kallon wasan, za ta riƙa lura da motsi, da dabarun ‘yan wasa, da haɗin gwiwar dake tsakanin shahararrun ‘yan wasa, da kuma ƙwarewarsu ta yin nazari wasan a fili, don ganin abin da za ta iya amfani da shi.

Bayan kallon manyan wasannin ƙwallon ƙafa na duniya, Shui Qingxia ta fara fahimtar nata kura-kurai, tana bullo da wani tunani, wato samun horo a ƙasashen waje da sanin al’adun ƙwallon ƙafarsu. A shekarar 1992, Shui Qingxia, wadda ta shafe shekaru 9 tana buga ƙwallon ƙafa, ta shiga ƙungiyar ƙwallon kafa ta Prema ta ƙasar Japan, kuma ta kasance daya daga cikin ‘yan wasan ƙwallon ƙafa mata na farko a ƙasar Sin da suka yi wasa a ƙasashen waje, tana da shekaru 26 na haihuwa kacal a wannan shekarar.

A ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Prima da ke ƙasar Japan, Shui Qingxia ta yi saurin zama jigo a ƙungiyar. Amma a shekara ta biyu da take a ƙasar Japan, Shui Qingxia ta ji rauni a wasan koyarwa da ƙungiyar wasan kwallon kafa ta maza, kuma aka saka farantin ƙarfe mai tsayin centimita 30 a cikin ƙafarta ta dama.

Bayan ta ji raunin, Shui Qingxia ta dawo ƙasar Sin, kuma bayan watanni 5 kacal, ta ɓulla a filin atisaye na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Shanghai.

Bayan ta murmure daga raunin da ta samu, Shui Qingxia, wadda ta shagaltu da horo da gasa, ba ta da lokacin damuwa da aikin tiyata, hakan wannan farantin ƙarfe ya zauna a ƙafarta ta dama har tsawon shekaru 7.

A cikin fiye da shekaru goma na buga wasan ƙwallon ƙafa, Shui Qingxia ba ta taba tsayawa saboda jin rauni mai tsanani ko maras tsanani ba, muddin tana tafiya a filin wasa, ta kan manta mene ne wahala da gajiya, tana ta guje-guje kamar ba ta jin zafin raunin da take jikinta. Kocin yana damuwa da ita kuma sau da yawa ya yi mata tsawa a wajen filin: “Ki rage gudu kuma ki huta kaɗan.”

Shui Qingxia

A shekarar 1994, Shui Qingxia ta koma cikin ƙungiyar ƙasar Sin, kuma ta halarci gasar wasannin Asiya karo na 12 da aka yi a birnin Hiroshima na ƙasar Japan a wannan shekarar, inda ta jagoranci ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Sin wajen lashe lambar zinare.

A cikin gasar cin kofin Asiya guda biyu da suka biyo baya, Shui Qingxia ta taimaka wa ƙungiyarta lashe gasar. A shekarar 1997, ta kuma lashe gasar cin kofin Asiya karo na biyar a sana’arta.

Ya zuwa yanzu, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta kasar Sin ta lashe gasar sau shida a jere tun bayan da ta halarci gasar cin kofin nahiyar Asiya a shekarar 1986, inda ta zama babbar ƙungiyar ƙwallon kafa ta mata ta farko a nahiyar. An kuma yi wa Shui Qingxia da abokan wasanta laƙabin “‘yan wasan zinare na ƙasar Sin”.

A shekara ta 2001, Shui Qingxia ‘yar shekaru 35 ta yanke shawarar “rataye takalmanta”. Har ila yau, ba ta da shirin barin wasan ƙwallon ƙafa, ta riga ta tsara makomarta: wato za ta zama koci.

Tunaninta na zama koci, ya fara ne tun Shui Qingxia tana matashiya, a shekarar 1999, kafin ta yi ritaya, ta fara halartar darussan zama koci, ta ce, “Tuni na yanke shawara cewa, ina son zama koci, don haka na fara yin shirye-shirye tun da wuri.”

Bayan ta zama koci, ta shafe kusan shekaru 10 a sassan horar da matasa na ƙasa ko na gida, kuma tana da zurfin fahimtar yadda ake horar da matasa, tsarin ɓangaren wasan da yanayin al’adu na sana’ar wasan ƙwallon ƙafa na mata. Ta bayyana cewa, “Jagorancin ƙungiyar matasa da ƙungiyar yara ya sa na ji cewa, neman ci gaban wasan ƙwallon ƙafa na mata na ƙasar Sin ba abu ne mai sauƙi ba, ‘yan mata da ke buga wasan ƙwallon ƙafa ba su da yawa, kuma iyaye ƙalilan ne ke son barin ‘ya’yansu su buga wasan ƙwallon Kafa, wanda hakan ke haifar da wahalar zabar ƙwararru a fannin.”

Matsalolin da Shui Qingxia ta gamu da su a shekaru 10 da suka gabata, su ne har yanzu masu horar da matasa suke fuskanta a shekarar 2022.

Shui Qingxia a tsakiyar fili

A shekarar 2010, Shui Qingxia ta koma birnin Shanghai, inda aka nada ta a matsayin mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta matasa mata ta Shanghai, kuma a shekarar 2011, ta jagoranci ƙungiyar ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ta mata ‘yan ƙasa da shekaru 17. Wannan shi ne kofin farko da Shui Qingxia ta lashe a matsayin koci.

A shekarar 2013, ta kai ƙololuwar aikinta na horarwa a hukumance. A shekarar 2014, ta jagoranci ƙungiyar lashe gasar ƙwallon ƙafa ta mata, kuma a shekarar 2015, ta lashe gasar cin kofin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Sin, da gasar wasan ƙwallon ƙafa mata ta Sin wato Women’s Super League, har ma da gasar zakaru ta ƙasa karo na 13.

A ranar 18 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, hukumar ƙwallon kafa ta ƙasar Sin ta fitar da sanarwar cewa, Shui Qingxia za ta zama babbar kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Sin. A wancan lokacin, kwanaki 63 kawai suka rage kafin a bude gasar cin kofin nahiyar Asiya.

Shui Qingxia ta ce, “Lokacin da na samu labarin nada ni, gaskiya na san zan fuskanci ƙalubale, na shafe sama da shekaru 30 a harkar ƙwallon ƙafa, kuma tunanin ƙwallon ƙafa na mata ya dade a cikin zuciyata, kuma a ko da yaushe ina son zama kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Sin.”

Har yanzu Shui Qingxia ba ta amince da shan kaye ba, ta ce, “Mutane da yawa na tunanin kafaɗun mata ba su da ƙarfin ɗaukar kaya, amma ko ƙungiyar za ta iya cin nasara ko a’a a gasa, wannan ba shi da alaka da jinsin kocin. Na taɓa riƙe wannan mukami, kuma na yi nasara, tun da na zaɓi wannan sana’a, zan zama mai samun nasara, kuma in nuna yadda masu samun nasara suke.”

Har yanzu Shui Qingxia tana iya tuna lokacin da ta fara ganawa da ‘yan ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafar mata ta ƙasar, a lokacin ƙungiyar tana jimamin kayen da ta sha a wasannin Olympics na Tokyo. Shui Qingxia ta ce, “Babban abin da take ji shi ne ƙungiyar ba ta yi imani da kanta ba. A gani na, wannan ba shi da kyau, dole ne in gyara tunanin ‘yan wasan ba tare da bata lokaci ba.”

A hirar ta ta farko bayan zama babbar kocin ƙungiyar ƙasar, Shui Qingxia ta gabatar da wata kalma, wato “’yan’uwa mata”. Tana fata ’yan ƙungiyar za su taimakawa juna kamar yadda ‘yan’uwa mata suke yi. Ta ce, “Ba wanda ke farin ciki lokacin da yake cikin koma baya, amma abu mai mahimmanci shi ne yadda za sauya wannan batu. Don haka, tun daga ganawarmu ta farko, na ƙarfafa wa kowa da kowa gwiwa, tare da fatan taimakawa dukkan ’yan ƙungiyar, ta yadda za su dawo da ruhun juriya da sha’awarsu ta samun nasara.”

Shui Qingxia

Ba da daɗewa ba, mun ga wannan canji a fagen gasar cin kofin Asiya, ƙungiyar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasar Sin ta lallasa Taipei ta ƙasar Sin da ci 4-0, Iran da ci 7-0, sai kuma Vietnam da ci 3-1, kana bayan da suke rashin nasara a baya sau biyu, sun kuma yi kunnen doki sau biyu, ƙungiyar ƙwallon kafar mata ta Sin ta kai wasan ƙarshen bayan ta doke Japan a bugun daga kai sai mai tsaron gida. A ƙarshe dai, tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Sin ta sake lashe kofin gasar Asiya bayan shafe shekaru 16, kuma ƙasar Sin gaba ɗaya ta shiga farin ciki da aka daɗe ba a manta ba, sanadiyar ƙwallon ƙafa.

Shafin yanar gizon Hukumar Ƙwallon Ƙafa Ta Asiya wato AFC a takaice ta taba yin sharhi game da Shui Qingxia: Ta fi kowa sanin yadda za a lashe gasar cin kofin Asiya ta mata.

Mutane na cewa, Shui Qingxia ta dawo da ruhi da halayyar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Sin, kuma ta sauya yanayi da tsarin ƙungiyar.

A baya jama’a na nuna shakku kan “Ko za ta iya ko ba za ta iya ba”, yanzu mutane suna fatan “Za ta samu nasara yadda ya kamata.” Shui Qingxia ba ta damu da abin da jama’a ke faɗa ba, abubuwan da take tunani har yanzu, abubuwa masu sauƙi kamar yadda take wasan ƙwallon kafa a yayin da take matashiya. Ta ce, “Ni ma ban sani ba ko zan iya ko ba zan iya ba, abu mafi mahimmanci shi ne, a daina wannan tunanin. Ina burin samun nasara, ina fatan ni da ƙungiyata za mu ɗan ƙara ƙwazo, ina son ƙara ƙaimi wannan karon fiye da baya, ta yadda za mu kai ƙungiyar ga nasara.”