Arewacin Nijeriya: Tauyayyun zakuna!

Daga MUHAMMAD NASEER LERE

Ba ƙaramin lamari ba ne ballantana a ce zai iya shiga rubibi har a manta. Na tabbata komai nisan lokaci ƙwaƙwalenmu ba za su iya mantawa da irin kisan gillar da ake mana a AREWA ba! Sannan ba za mu iya hana bakunanmu faɗin, An kasa ceto rayukanmu ba. Ina tunanin muna faɗin hakan ne domin kunnuwanmu sun ji lokacin da gwamnatinmu ke rantsuwar tsare rayukanmu.

Kenan, ba za mu iya daina faɗin, an kasa ceto rayukanmu ba, har sai ranar da muka manta da kalaman gwamnati na alƙwarin tsare dukiya da rayukanmu. Ko dai mu ce an kasa ceto rayukanmu, ko mu ce an kasa tsare duniyarmu, ko mu ƙi cewa, ƙarshe dai dole ko’ina a faɗin Duniya an fahimci yadda farashin rayukan bani Adama ya zama abu mafi arha a Arewa.

A gefe guda, kowa ya san yadda mu (‘yan Arewa) Muka rikirkice. Duk da rikicewarmu ba ta hana shige da fice, da cigaba da tasirin kashe-kashen da ake aikatawa ba, amma ƙalilan cikinmu sukan iya zub da hawaye a duk lokacin da wani gidan jarida ya binciko wata ta’asa wacce masu iko da aikata ta’addancin suka aiwatar ta fyaɗe ko mummunan kisan gilla.

Duk da mun kasance a gaba-gaba wajen surutu a kafafen watsa labarai a Duniya, amma abin mamakin shi ne, surutun mamayar yankin Arewa ya zama abinda ya fi kowanne surutu samun ƙarancin sharhi. Ƙila hakan ya samo asali ne sakamakon yadda muka rikice muka kasa gane bakin zaren wannan mummunan lamari wanda tuni ya zautar da ƙwaƙwalen mafi yawa daga cikinmu!

Haƙiƙa, wannan lamari ya kasance abinda yafi cinye mana tuwon ƙwaryarmu. Musamman lokacin da muke kasa amsa tambayoyi daga maƙwabtan ƙasashenmu a kan musabbabin abinda ya jawo wannan shiririta. Dole haka za mu amsa matsayin da suke bamu na rashin damuwa da lamarin da yankinmu na Arewa ke ciki. Da yake suna ganin yadda kullum muke rubutu a yanar gizo cikin farin ciki da annashuwa alhalin a dai-dai lokacin ana labarin an tare mota an ƙone kowa, ciki kuwa har da mace me ciki, har jaririn an ƙone shi. Ƙila wannan labarin ya cancanci kowa ya shiga taitayinsa a yankin da ba sunan sa Arewa ba.

Ashe lokacin da muke iya kwana cikin gidajenmu a Arewa ɗin da muke ciki akwai yan gudun hijira dubbai da suke kwana a gefen tituna. A cikin lamarinsu ba wai magana ake a kan gurin kwana ba, ana magana ne a kan ya zuciyar da ke tunanin yadda aka kashe danginta za ta samu ta ci abinci ko da sau ɗaya ne a wuni? In muka duba, a yadda muke ba abin mamaki ba ne, don mun kasa ɗaukar lamarinsu da muhimmanci. Amma abin mamakin shi ne, ta ina ake samun masu bibiyar matansu da harshe a zare da miyau? Na tabbata ko da muna da ɗabi’ar lusaranci! Amma babu wanda ya san mu da ɗabi’a irin ta birrai.

Menene duk ya jawo waɗannan irin abubuwan al’ajabi? Wataƙila a gurin wasu wannan tambaya ce me sauki. Amma mu dai rikita-rikitan dake damun mu, ba za ta ba wa wannan tambaya amsuwa ba. Shin ashe amsar tambayar wanda cikinsa ya ƙulle zai wahala haka? To koda dai ba zai iya cewa cikin sa na ciwo ba, lila hannunsa zai nuna amsar sa. Amma mu dai ga ciwon, amma sai dai mu bebaye ne, gashi kuma mu makafi ne, hakazalika, hannuwanmu sun ruve, babu hanyar da zamu iya bayyanar da ainihin cutar dake damun mu. Wala Allah sai ranar da ƙawa zuci ya fara fitowa a cikin sura ta zahiri, to ina tunanin Wannan ciwon namu zai samu waraka. Ƙila kuma lokacin sai dai ‘ya’yan jikokin yaranmu su ci moriya.

Duk da cewa zahirinmu ya nuna ba mu san ta inda za mu magance matsalar rashin tsaro dake addabarmu ba, amma fa a ƙarƙashin zuciyar wasunmu akwai mafitar dukkan matsalolinmu, sai dai tsoro da wariyar jinsinmu ya zama wani babban shamaki wanda shi ne asalin abinda zai sa mafitar ta cigaba da wanzuwa a zuciya. Saboda sun gwammace zama cikin salama fiye da zama cikin zargi da zagi daga alƙaluman ‘yanuwansu.

A maimakon mu gyara ɗabi’ar, sai muka gwammace mu ɗauko duk nauyin, mu jibga wa gwamnati. Duk da cewa haƙƙin gwamnati ne ta ba mu tsaro, amma babu yadda za ta iya shiga zuciyarmu ta gyatta mana ita, kuma babu yadda za a yi gwamnatin ta mai da hankalinta a kanmu, alhalin ba mu da ƙarfin zuciyar tunkarar ta, mu faɗa mata abinda ke damun mu. To ya za a yi kenan? Gwamnatin ba za ta iya gyara mu ba, gashi kuma sai mun gyarun kafin ta iya yi mana magani. Amma tsakaninmu da gwamnatin ba kamar marar lafiyar da ya ƙi zuwa asibiti ba ne.

Tunda har mun kasa gyarawa ɗin, menene abinda ya rage a zargin gwamnati? Kamar yadda uwa ke ba wa jariri ruwa idan yana kuka ba tare da ta san haƙiƙanin abinda ke masa ciwo ba, haka gwamnati ke yi mana albishir xin samun garaɓasar fasahar sadarwar 5G. Kamar yadda jaririn ba ruwa ƙila yake buƙata ba, haka muke mu ma, ƙila mun fi buqatar rayuwa cikin gidajenmu da fasahar 2G fiye da rayuwa cikin kaburburanrmu da fasahar 5G.

Amma kamar yadda jairiri ba shi da bakin cewa, “ni ba ruwa nake buƙata ba, maganin ciwon ciki nake buƙata,” haka mu ma muka rasa bakin da za mu ce wa gwamnatinmu,“mu fasahar rayuwa muke Buƙata, ba fasahar sadarwa ba.” Wataƙila za ku ce, ai ministoci, ‘yan majalisu da sauran wakilanmu suna faɗa wa gwamnatin ko? To ku ɗauki abinda suke faɗa wa gwamnati dangane da matsalarmu kamar kukan jaririn.

Gashi dai mahaifiya ta san kuka alamun matsala ne, amma ba ta fahimtar yaren jaririn, ballantana ta gane ainahin abinda ke damun sa. Idan za mu yi adalci, ba za mu ce ba sa isarwa ba, amma kuma ba a fahimtarsu. Mu ne dai za mu iya yin yaren da za a fahimce mu, amma girman kai irin namu ya hane mu koyon yaren daga wararrun cikinmu. Ba wai ma mun ƙi koya ba ne kawai, a’a duk lokacin da a buƙaci himmarmu, babu amsar da muke da shi sai zagi, da ƙoƙarin yahudantar da lamarin.

Ana cikin haka, sai wasu suka bar guraren dafa abinci na gidajenmu suka zo suka ce mana, tunda dai su wakilanmu muryarsu ta koma ta jarirai ba za a iya fahimtar su ba, me zai hana mu, mu zama irin jarirai masu ciwon cibiya ɗin nan? Kunga ko ba mu yi kuka ba, in tabon kumburin cibiyar ya bayyana za a gaggauta nema mana magani. A ƙalla dai mun bayyana ciwon.

Lamarin nan akwai al’ajabi, wato akwai wata mu’ujiza wacce Allah ya hore mana. Wato duk da kasancewarmu masu buƙatar ganin an daina zubar da jini a Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto, Borno Neja, Jos da sauran guraren da ake zubar da jinin Hausawa da Fulani, amma har muna da lokacin zaɓar hanyar da ta yi dai-dai da ra’ayinmu. Har muka gwammace tsine wa duk wanda yace mu yi abu kaza, domin ceto rayukanmu. Kamar yadda wasunmu suka cewa waɗanda suka baro digajensu, da nufin tunkarar matsalarmu, karuwai, wasu kuma suka gwamnace su basu matsayin yaran yahudu fiye da addu’ar Allah ya dafa musu.

A dai-dai wannan lokacin sai masu hankali suka fara tunanin, anya matsalar nan, ba matsalar kai da kai ba ce? Wato wasu har sun fara tunanin, wannan matsalar ba wasu ne suke rurutata ba? Sai masu kukan samuwar ta. Kun ga fa yadda sakacinmu ya jawo mana zargi daga masu hankali.

To ya muka iya? Ana maganar ana kashe-kashe, mu kuma muna maganar, bai kamata mata su ce, a fito titi don kawai ana kashe wasu ba. Wannan shi ne ya sa masu hankalin can suke ganin kamar mu ne matsalar kanmu da kanmu, har suke ganin kuma mu ne kuma maganin matsalar. Sannan me ya kawo maganar karuwanci da yahudanci, alhalin ana maganar yadda kukan marayu ke wara yaiwata ne a Arewa?

Kwatsam! Sai wasu jarumai (Ƙila a gurina ne) Amma na fahimci hankalina ne ya kasa ba su matsayin da yan Arewa suke basu na ballagazanci domin ko ba komai cikinsu akwai waɗanda nake gani tamkar mahaifiya. Suka fara aikata abinda suke kira a kai zahirin ganin idanun Duniya. Wai me suka ce har suka fuskanci rubdugun jahiliyya? Na san za ku girgiza idan kuka ji cewa, mata ne suke kiran mazan gaske su fito domin yin zanga-zangar lumana. Wannan lalacewa har ina haka? A ce mata sun fito daga madafar abinci alhalin ga mu nan mazaje masu jiran ko-ta-kwana.

Tun karon na farko da Malama Rahma Abdulmajid ta bayyana lamarin Arewa a matsayin abinda ya fi ƙarfin a zauna a gida a yi addu’ai, hankalina ya tashi matuƙa. Ban samu damar duba rubutunta ba, kamar yadda na samu damar karanta sharhin masu tofa albarkacin bakinsu a ƙasan wallafar tata ba. Abinda ya ba ni alfahari har sai da na mance da abinda ake tattaunawa shi ne, yadda naga tarin malamai da muke dashi a Arewa musamman Duniyar fesbuk. Ko kun san cikin ‘yan mintuna suka kora mana ita daga gidanmu na gado? Sun zama masu ruwa da tsaki cikin Musluncinmu cikin sauƙi.

Duk da wannan irin fatawowi da suka samu bayyana rana tsaka, hakan bai hana Malama Rahma Abdulmajid cigaba da haɗa tawagarta ba. Wai ma anya kuwa ‘yan Arewa sun saba ganin irin wannan jarumtar daga gurin mata? Domin kowa a Arewa masani ne a kan mace halitta ce mai matuƙar raunin da ko girki kawai saboda ibada ce, amma da ragwancin mace ba zai bar ta ta iya girkin ba tsabar rauni. Sai gashi mata na shirin yi wa wannan dogon tarihin terere.

Cikin lokaci tawagar ta fara ba mu mamaki, duk da guruf na Wasaf din da aka buɗe da farko abin dariya ya zama, amma da yawa cikin waɗanda suke dariyar sun fahimci lallai fa yau tauyayyun hallitu za su zama zakuna. Ko ba komai yau za a fara ganin zaki da ɗan kwali a Arewa. Wannan ai tarihi ne babba. Cikin ikon Allah lamari ya fara kankama, inda wasu manyan Arewa suka fara nuna goyon bayansu ga waɗannan tauyayyun iyayen zakuna namu.

Sai gashi duk wata ɗabi’ar da muke tauye su da ita ta zama makami, wajen bayyanar da ciwon dake damun su na irin mummunar ɓarnar da ake a Arewa . In zan iya tunawa ko a firamare ana yawan tsokanar mata da saurin zubar da hawaye, za ka ji an ce, mata abu kaɗan yake saka su kuka, wato basa iya shanye ƙunci, inji mu.

Wannan ne ya sa tausayin mata irin su Zainab Ahmad (Bint Hijazi) ya bayyana qarara, domin ko ‘yan jaridar da suke ɗaukar rahoto sautin kukan ta ya taɓa musu zuciya. To ina kuma ga masu jiran ganin, lamarin na wasa ne ko na siyasa? Sautin kukan yana bayyana yadda ake tare mata ai musu fyaɗe a Arewa. Hakazalika, a cikin kukan nata, za ka iya jiyo sautin kukan wacce aka kashe mijinta, aka kashe iyayenta aka ƙyale ta da marayun da ba ta da yadda za ta ciyar da su. Allah Sarki, lamarin abin tausayi.

A haka wannan lamari ya cigaba da tafiya har ranar da alƙawarin tawagar Rahma Abdulmajid ya cika. Sai ga Zahra’u Ibrahim ta jawo tawagarta daga Kano, sai muka hango irin su, Nadiya Ibirahim Fagge, Zainab Naseer Ahmad da sauran ‘yanuwa mata da za mu iya yaba wa ƙoƙarinsu na ganin ba su kunyata ikrarin da suke ba. Duk da cewa an fito zanga-zangar a abuja, amma fitowar kano tafi kowacce jan hankali da izza. Fitowa zanga-zangar neman a bawa Arewa tsaro tayi tasiri sosai, ko ba komai, mun fahimci mata na iya kawo abinda zai iya tasiri ganin ido.

Fitowar mata a tituna da poster ɗauke da ‘SecureNorth’ ya samar da tattaunawa da yawa kafafen sadarwa, amma wanda suka fi ɗaukar hankali sune;
Shin zanga-zanga za ta kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Arewa?

  1. Sannan me ya sa mata za su fito zanga-zanga?
  2. Shin wai zanga-zanga a muslunci ba haramun ba ne?
    Amma wanda aka fi tattaunawa shi ne, zanga-zanga ba zai ba
    zai kawo mafita a Arewa ba. Duk masu maganar suna kawo hujjar cewa, addu’a ta wadatar ne, babu buwatar sai an yi zanga-zanga. Kamar yadda Mawaqi Nura M Inuwa ya bayyana wa masoyansa cewa, ba zai fito zanga-zanga ba, gudumawar da zai iya bayarwa addu’a ce, ta wuce a ce mata kawai. Amma ko shi Nura ɗin cewa ya yi bai ji daga manya ba, bai ji an faɗi a masallacin juma’a a fito zanga-zanga ba. Wataƙila da wanin liman zai ce a fito, to ƙila shi ma zai fito.
    Wannan shi ne haƙiƙanin abinda ya fi raunana masu irin ra’ayina. Saboda kai tsaye an bayyana mana cewa, su fa malamai da limananmu ba su ma damu da mummunan halin da muke ciki ba Domin sun kasa cewa komai, sun kasa yin komai, sannan sun kasa bayyana wa al’umma cewa bayan addu’a akwai wani matakin da ake bi wajen daƙile yanayin zalunci da danniya, wanda musluncin da suke koyarwar ya yi nasara ne dalilin bin matakin.

Kenan ya kamata su nuna cewa, inda a ce addu’a ake buƙata ba tare da motsawa ba, da yanzu babu labarin yaƙin Badar, wanda Manzon rahma (SAW) ya fita tare da Sahabbansa domin ceto martaba da ƙimar addininmu. Wannan ya ƙara tabbatar da a wannan yanayin ko dai ka zo a yi da kai, ko ka koma gefe ka yi shiru ka zura idanu. Amma duk wata kalma da za ka furta za ta iya juyawa zuwa wani lamarin na daban.

Bayan fitowa zanga-zanga, za mu tafi zuwa abinda ya faru bayan fitowa zanga-zangar, wanda za mu leƙa sati mai zuwa idan Allah ya nufa muna numfashi.

Muhammad Naseer Lere ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto daga Kaduna. 0701 485 0068