Tsaftace yadda matasa ke amfani da zaurukan sada zumunta

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ƙarshen makon da ya gabata na samu halartar wani babban taron bita na yini biyu da ƙungiyar matasan Arewa masu amfani da zaurukan sada zumunta don isar da saƙonni, yaɗa labarai da tallata kayayyakin su na kasuwanci ta gudanar. Ƙungiyar da aka fi sani da suna Arewa Media Writers, ta shirya gagarumin bikin cika shekaru biyu da kafuwar ƙungiyar ne a garin Bauchi, wanda ya gudana a babban Hotel ɗin nan na Zaranda.

Matasa daga dukkan sassan jihohin Arewa sun samu halartar wannan taro, wanda aka yi wa taken ‘Rawar Da Kafofin Sada Zumunta Ke Takawa Ga Cigaban Arewa, A Ɓangaren Tsaro, Siyasa Da Zamantakewa’. Yayin taron bitar wanda aka fara gudanar da shi tun ranar Jumma’a 15 ga watan Yuli, kuma aka kammala da bukin cika shekaru biyu da kafuwar ƙungiyar a ranar Lahadi 17 ga wata, an faɗakar da ‘ya’yan ƙungiyarsu fiye da 500 kan aikin samar da bayanai da yaqi da yaɗa labaran ƙarya a kafofin sadarwar zamani, da kuma haɗa kan matasa wajen yin magana da murya ɗaya kan duk wani al’amari da ya shafi yankin Arewa da al’ummar ta da ke zaune a sauran sassan ƙasar nan.

Ƙungiyar ta gayyato mashahuran malamai, fitattun ‘yan jarida da masu faɗa a ji a harkokin watsa labarai, waɗanda suka koyar da matasan kan hanyoyin yaqi da labaran ƙarya a kafofin sada zumunta. Yadda ake rubutu da aikin jarida, na yaɗa labarai a kafofin sada zumunta. Tasirin kafofin sada zumunta a siyasar Nijeriya, tsaron ƙasa, da amfanin ta ga al’umma.

Sauran darussan da aka duba sun haɗa da yadda ake neman kuɗi, da aiki a kafofin sada zumunta. Tasirin haɗin kan marubutan Arewa, da kuma muhimmancin harshen uwa, ga tasirin hulɗa da jama’a a yanar gizo.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamred Abba Sani Pantami ya bayyana cewa a tsawon shekaru biyu da ƙungiyar ta yi ta daɗe a matakin jikohi da rassa tana shirya taruka don horar da matasa dabarun amfani da kafafen sadarwa na zamani da yadda za su ci moriyar su a ɓangarorin ilimi, kasuwanci da aikin jarida, har ma da shirya gasa a tsakanin marubutan adabi da Insha’i ƙarƙashin jigon da ya shafi tsaro, kare martabar al’adun Arewa da zaman lafiya.

Waɗannan duka darussa ne masu matuƙar muhimmanci da tasiri ga cigaban rayuwar matasan Arewa da ma ƙasa baki ɗaya. Kuma na yarda da bayanin da shugaban ƙungiyar na ƙasa inda ya ce, wannan taro shi ne irin sa na farko a matakin ƙasa da wata ƙungiya a arewacin ƙasar nan ta taɓa shiryawa da nufin ƙara gogar da ‘yan qungiyar waɗanda akasarin su marubuta ne, ko dai na littattafan adabi na Hausa, rubuce-rubucen fadakarwa a zaurukan sada zumunta, ko kuma ‘yan jarida ne masu shafukan wallafa labarai a kafofin sadarwar zamani, har ma da ma’aikatan watsa labarai daga sanannun tashoshin rediyo da talabijin daga jihohin Arewa.

Manajan sashin labaru da al’amuran yau da kullum na tashar rediyon Vision FM a Gombe, Malam Aliyu Abdu ɗaya daga cikin manyan baƙi a wannan taro ya shaida muhimmancin da shirya irin wannan bita ke da shi ga kyautata zamantakewa da rayuwar matasa inda ya ke cewa, shirya bita lokaci zuwa lokaci zai ƙara taimakawa wajen faɗakar da matasa yadda ya dace su yi rubutu da zai ɗauki hankalin magabata da gwamnatoci, da kuma amfani da ƙa’idojin rubutu yadda ya kamata.

Ra’ayin sa ya zo daidai da na ɗaya daga cikin waɗanda suka gabatar da lacca a taron Malam Isma’il Karatu Abdullahi, shugaban kamfanin jaridar Hausa Daily Times wanda ya koka game da yadda ƙarancin ilimin aikin jarida ya sa wasu matasan da ke da son zama ‘yan jarida ke garajen yaɗa labarin da ba su san sahihancinsa ba wanda hakan ke sa labaran ƙarya saurin yaɗuwa a shafukan sada zumunta, da waɗannan matasa ke amfani da su. Malam Isma’il da Malam Aliyu na ganin duk da yadda hankalin mutane yanzu ya fi karkata ga zaurukan sada zumunta, domin neman labari, karatu ko isar da saƙonni, lallai ya kamata gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu su sa ido sosai tare da bai wa irin waɗannan matasa horo da tallafin da ya kamata, ta yadda za a iya cin moriyar ƙwazon da suke da shi, kawar da labaran ƙarya, da kuma samar da ayyukan yi.

Shi ma a nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers na Babban Birnin Tarayya Abuja, Abubakar Baban Kyauta ya bayyana buƙatar samun goyon bayan gwamnati da hukumomin gwamnati wajen amfani da damar da waɗannan matasa ke da ita ta mallakar shafukan watsa labarai da ke da dubban magoya baya waɗanda ke bibiyar ayyukan da suke yaɗawa, da ba su kwangilolin ayyuka na faɗakarwa, isar da saqonnin da hukumomi ko ma’aikatun gwamnati da na masu zaman kansu wanda ake son isarwa ga jama’a, domin hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa da dagewa kan abin da suke yi a matsayin sana’a, da kuma gudunmawarsu ga cigaban ƙasa da zaman lafiya.

Ya koka da yadda wasu ‘yan siyasa da ya kira da marasa kishin cigaban matasa, ke amfani da wasu masu irin waɗannan shafuka suna taimaka musu wajen yaɗa manufofinsu na siyasa, amma ba sa tallafa musu yadda rayuwarsu za ta inganta, su samu kayan aiki na zamani ko ofisoshin gudanar da ayyukan su. Sai dai su je suna kashe maqudan kuɗaɗe wajen ɗaukar nauyin jaridun ‘yan Kudu da ba su damar gina jaridun su, alhalin ba za su tsinana musu komai ba, idan lokacin zaɓe ko buƙatar kare mutuncinsu da na al’ummar Arewa ya taso ba.

Wannan ƙorafi na Baban Kyauta na daga cikin abubuwan da suka daɗe suna ci wa waɗannan matasa tuwo a ƙwarya, yana ma daga cikin manufofin da suka ga ya dace su haɗa kai, don amfani da murya guda, musamman a daidai wannan lokacin da ake tunkarar Babban Zaɓen 2023, inda siyasar kowa-tasa-ta-fishshe-shi ta ke girgiza ‘yan siyasa, sakamakon yadda a zaɓukan baya aka riƙa fakewa a bayan sunan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ana cin zaɓuka a ɓagas! Yanzu kuwa dole sai ɗan siyasa ya tashi tsaye ya yi aiki a ƙasa, kuma ya jawo jama’ar sa a jiki ya yi aiki da su. Wannan ba zai wadatar ba a wannan zamani sai da matasa ‘yan boko masu wayewa kan zaurukan sada zumunta, don yaɗa manufofinsa.

Ɗan jarida kuma Daraktan sashin labarai na jaridar Dimukraɗɗiyya a yanar gizo, Malam Shu’aibu Abdullahi yana ganin cewa ya kamata matasa masu shafukan yaɗa labarai na yanar gizo su riƙa kusanta da neman shawarwarin ‘yan jarida na sosai waɗanda suka qware a aikin don neman shawarwari kan yadda za su ci moriyar aikin jarida da kuma yaɗa labaru masu inganci.

Daga cikin irin waɗannan matasa da ake ta magana kansu akwai sakataren ƙungiyar Arewa Media Writers na Jihar Filato Muhammad Zakariyya Musa wanda ke da shafin Jasawa Daily News wanda ya bayyana matuƙar farin cikinsa da irin darussan da ya koya a wajen wannan taron bita, da yadda za su inganta ayyukan da suke gudanarwa a zaurukan sada zumunta.

Wani al’amari mai ɗaukar hankalin ‘yan Nijeriya, musamman gwamnatoci da masu nazarin abubuwan da ke faruwa a zaurukan sada zumunta shi ne yadda ake amfani da zaurukan wajen yaɗa bayanai masu sosa zuciya da suka shafi addini, ɓangaranci da siyasa. Abubuwan da wasu matasa ke rubutawa suna da ɗaga hankali sosai, domin yadda hakan ke iya tunzura wasu da sanya ƙyamar wani ɓangare ko addini, saboda kawai bambancin siyasa ko al’adar tafiyar da rayuwa.

Ƙalubale ne a kan gwamnatoci da hukumomi su riƙa shiryawa matasa bita da horar wa, domin ƙara faɗakar da su muhimmancin kishin ƙasa, zaman lafiya da mutunta bambance-bambancen da ke tsakanin ‘yan Nijeriya. Ita ma ƙungiyar Arewa Media Writers da ta yi wannan taro bayan yabo da jinjina, muna kuma ƙara ƙarfafa mata gwiwa ta cigaba da shirya bitoci irin haka, domin rage taɓargazar da wasu matasa ke yi a zaurukan sada zumunta, suna cin mutuncin shugabanni, yaɗa bayanan ƙarya, da tunzura juna don haifar da ƙiyayya da rashin zaman lafiya.

Yanzu da gwamnati ta ɓullo da dokoki game da yadda ‘yan Nijeriya ya kamata su yi amfani da zaurukan sada zumunta, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su haɗa kai da ƙungiyoyin matasa irin su Arewa Media Writers, domin shirya tarukan ƙara wa juna sani da faɗakarwa game da tanade tanaden dokar da yadda za su yi wa sauran ‘yan ƙasa bayani ta cikin shafukansu, don saƙon da ake nema ya samu isa ga jama’a cikin hanzari, kuma harshen da kowa zai gane ya fahimta.