Abu Zubaydah da aka yi wa laƙabin “daɗaɗɗen fursuna”

Spread the love

Daga MINA

Abokai, yau “duniya a zanen MINA” na zana wani mutum mai suna Abu Zubaydah, da aka yi wa lakabi “dadadden fursuna” dake tsare a gidan yarin Guantanamo. Hukumar leƙen asiri ta Amurka ta mai da Abu Zubaydah a matsayin “mutum mafi daraja dangane da batun ta’addanci”, amma ana tsare da shi ba tare da kai masa ƙara ko yanke masa hukunci ba, inda ake azabtar da shi har tsawon shekaru 20, duk da cewa an taba gabatar da shaidu cewa, shi ba mambar ƙungiyar Al-Qaeda ba ne.

Bisa ƙididdigar da asusun Open Society Foundations na Amurka ya bayar, hukumar leƙen asiri ta Amurka ta kafa irin gidajen kurkuku waɗanda su kan keta haƙƙin Bil Adama a kimanin kasashe da yankuna 54 na fadin duniya, a yayin da mutanen da aka ci zarafinsu sun kai a ƙalla 136.

Amurka mai matuƙar nanata muhimmancin kare haƙƙin Bil Adama, ita ma tana yiwa kanta laƙabin “Mai kare haƙƙin Bil Adama”, amma ta yi biris da haƙƙin Bil Adama na mutane irinsu Abu Zubaydah, to ko haƙƙin Bil Adama a ganin wasu ‘yan siyasar Amurka na da fuska biyu?

Mai zane: MINA

By Editor