An miƙa lambar yabon zaman lafiya ta MƊD ga sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura wa Kongo(Kinshasa) karo na 25

Spread the love

Daga CMG HAUSA

An mika lambar yabon kiyaye zaman lafiya ta MƊD ga dukkanin sojojin kiyaye zaman lafiya su 218, da ƙasar Sin ta tura wa ƙasar Kongo (Kinshasa) karo na 25, a sansaninsu dake jihar South Kivu ta kasar a jiya Litinin.

Bisa umurnin tawagar wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Kongo ta MƊD ko MONUSCO a taƙaice, an shirya bikin mika lambar yabon ga sojojin kiyaye zaman lafiya da ƙasar Sin ta tura wa ƙasar a karo na 25 jiya, inda kwamandan rundunar sojojin Deng Liang ya bayyana cewa, dukkanin sojojin ƙasar Sin sun darajanta yabon da ake yi musu, kuma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, domin ba da gudummowarsu ga wanzar da zaman lafiya da bunƙasuwar duk duniya.

Tun bayan da sojojin suka fara aiki a ƙasar a watan Oktoban shekarar bara, dukkaninsu sun nuna kwazo da himma wajen warware matsaloli iri daban daban da ake fuskanta, haka kuma, likitocin tawagar jami’an kiwon lafiya ta kasar Sin, sun samar da tabbacin aikin likitanci ga jami’an tawagar MONUSCO, waɗanda yawansu ya kai sama da 4000.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa

By Editor