Tagwayen titunan mota na ƙasar Sin sun haɗe kaso 95 bisa ɗari na alummun ƙasar

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Ƙasar Sin ta kafa ƙaƙƙarfan ginshiki a fannin gina manyan titunan mota, domin haɗe sassa daban daban na yankunan ƙasar, da sauƙaƙa zirga zirgar ababen hawa, kuma tuni waɗannan manyan tituna suka haɗe kimanin kaso 95 bisa dira na yankunan ƙasar.

Da yake karin haske game da hakan, yayin wani taron manema labarai a jiya Litinin, jamii a ma’aikatar sufuri ta ƙasar Wang Tai, ya ce a yanzu haka, manyan hanyoyin ƙasar sun haɗe kaso 98.8 bisa dari na birane masu yanwan alummar da suka zarta 200,000, da manyan yankunan gudanarwa, yayin da irin waɗannan manyan tituna suka game kusan kaso 88 bisa dari, na sassan dake da matsayi na gunduma.

Wang ya ƙara da cewa, manyan hanyoyin mota dake ƙasar Sin sun hade dukkanin yankunan gudanarwan dake sama da matsayin gunduma, da ɗaukacin masu iyaka da tashoshin ruwa da ake amfani da su a duk tsawon shekara.

Ya ce ya zuwa ƙarshen shekarar da ta gabata, gwamnatin ƙasar Sin ta gina tagwayen hanyoyin mota da tsayinsu ya kai kilomita 117,000, inda kuma aka buɗewa matafiya manyan titunan mota da tsayinsu ya kai kilomita 257,700.

A farkon shekarar bana, mahukuntan ƙasar Sin sun fitar da wata takardar sanarwa, dake bayyana burin gina manyan hanyoyin mota na ƙasa nan da shekarar 2035, da za su kai tsayin kilomita kusan 461,000, waɗanda za su kunshi tagwayen hanyoyi masu tsayin kilomita 162,000, da manyan tituna dake haɗe manyan sassa masu tsayin kilomita 299,000.

Mai Fassarawa: Saminu Alhassan

By Editor