Gwagwarmayar Hajiya Gambo Sawaba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An haifi Hajiya Gambo Sawaba a ranar Lahadi, 15 ga watan Fabrairu na shekarar 1933, a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Sunan mahaifinta Isa Amartey Amarteifio (Christened Theophilus Wilcox,) ɗan asalin ƙasar Ghana ne. Ya kammala karatunsa a makarantar Ghana School of Survey. Ya yo hijira zuwa Nijeriya ne a shekarar 1910, ya zo ne don neman aiki a Nigerian Railway Corporation, daga nan kuma sai ya yanke shawarar yin zama na dindindin.

Aiki ya kawo shi garin Zariya, inda a nan Christened Theophilus ya karɓi addinin Musulunci, ya sauya suna zuwa Isa. A nan kuma ya haɗu da Fatima, wadda ta ke Banufiya ce ’yar asalin ƙaramar hukumar Lavun da ke jihar Neja. Kakanta maƙeri ne, jajirtaccen namijin da baya juya baya ga abinda ya sanya a gaba. Shi ne ya haifi mahaifinta (wato kakan Gambo Sawaba, Mamman Dazu).

A lokacin da suka haɗu, Fatima ta kasance Bazawara, tana da ’ya’yanta uku da suka haifa tare da tsohon mijinta mai suna Muhammad Alao, wanda ya rasu.

Bayan ’yan shekaru da haɗuwarsu sai suka yi aure, wanda a cikin auren nasu sun samu ’ya’ya shida, Gambo ita ce ’ya ta biyar. Asalin sunanta shi ne Hajaratu, ana kiranta da sunan Gambo ne saboda an haifeta bayan an haifi ’yan biyu kafin ita. Bisa al’adar Hausawa ana kiran wanda aka haifa bayan an haifi ’yan biyu da sunan Gambo, don haka ake kiran Hajara da sunan Gambo.

Karatu da rayuwa;

Gambo ta yi karatu a makarantar Native Authority Primaary School da ke Tudun wada Zariya. Daga nan karatunta ya tsaya, bayan rasuwar mahaifinta a shekarar 1943, wanda ya rasu sakamakon matsanancin ciwon kai. Shekaru uku bayan rasuwar mahaifinta, mahaifiyarta ma ta rasu.

Gambo tana ’yar shekaru goma sha-uku a duniya ta auri wani tsohon soja mai suna Abubakar Garba Bello, wanda ya samu kwarewar aiki, kuma ya yi ritaya bayan an gama yaqin duniya na biyu. Mijin Gambo Sawaba ya tafi ya barta a lokacin da ta samu cikin farko, kuma bai sake waiwayarta ba, har ta haifi ’yarta mai suna Bilkisu.

Bayan wasu ’yan shekaru, sai Gambo ta sake yin wani auren, inda ta auri wani mutum mai suna Hamidu Gusau. Mutum mai tsaurin ra’ayi da saurin fushi da tsangwama, wanda shi ma zaman nasu bai dau lokaci mai tsawo ba suka rabu. An ce bayan wannan auren ma ta sake yin wasu auren har sau biyu.

Gwagwarmaya da siyasa;

Gambo, tun a lokacin ƙuruciyarta mace ce mai tsayuwar daka a kan duk abinda ta sanya a gaba, tare da watsar da komai don ganin ta cimma gacin abin. Kuma da wuya a kayar da ita a magana ko musu a kan abu, matuƙar tana da gaskiya, ba ta yarda ta sarayar da haƙƙinta. Ba ta da ƙwauron-baki.

Ta taso da tausayin mutane masu taɓin hankali, tana zama da su, ta yi hira da su. Tana taimaka musu da abubuwan buƙata kamar su abinci, sutura da ’yan kuɗi idan tana da su. Har ma a kan yi faɗa da ita don kare haƙƙinsu.

Gambo ta fara fuskantar wahala a sha’anin siyasar Nijeriya tun tana da shekaru sha-bakwai a duniya. A wancan lokacin a Arewacin Nijeriya jam’iyyar da ta ke da ƙarfi ita ce N.P.C wato Northen People’s Congress, wacce ta ke da goyon bayan sarakuna da kuma Turawan mulkin mallaka.

Amma a tare da hakan, sai Gambo ta zaɓi ta shiga jam’iyyar adawa ta malam Aminu Kano, wato Northern Element Progressive Union, NEPU. Jam’iyya ce ta talakawa, wadda talakawan ne ke ɗawainiya da ita, ta hanyar sadaukarwa da kuma karo-karo, har ta yi ƙarfi.

Babbar manufar jam’iayyar NEPU ita ce; yaƙi da turawan mulkin mallaka, ba wa mata cikakkiyar damar fitowa a dama da su a harkokin karatun addini da na zamani, da harkar tattalin arziki da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Gambo ta shiga Jam’iyyar ne a lokacin da aka buɗe qaramin ofishin jam’iyyar a garin Zariya. A lokacin jam’iyyar na yin tarukanta a ɓoye, tare da voyewa hukumomi duk wasu aikace-aikacenta, (qila saboda gudun fushin sarakunan lokacin).

Kalmar ‘Sawaba’ ba ya daga cikin sunan Gambo na yanka, ko na dangi. Suna ne da ke nufin ’Yanci, ko kuma kuɓuta daga cikin wani hali na matsin-lamba. A wata majiyar an ce Malam Aminu Kano ne ya sa mata sunan bayan an zaɓe ta a matsayin shugabar matan jam’iyyar. Yayin da a wata majiyar kuma aka ce; ta samu sunan ne a yayin gudanar da wani taron siyasa a garin Zariya, yayin da wani mutum, ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar mai suna Alh. Gambo Sawaba, wanda kuma shi ne babban mai jawabi a taron, cikin barkwanci ya kirata da suna “Hajiya Gambo Sawabiya!”

Ta samu damar zuwa garin Abeokuta, inda ta ziyarci fitacciyar mai fafutukar kwatar ’yancin matan nan, wato Funmi-Layo Ramsome Kuti. Gambo Sawaba ta samu ilimi a kan hanyoyin da Funmi-layo ta bi ta samu nasara a zanga-zangar da ta shirya ta dakatar da harajin da matan garin Egba ke biya. Ta kuma samun ƙarin ilimi da dabarun zama ’yar gwagwarmaya. Ta fara da fafutukar yaƙi da auren wuri da ake yi wa ƙananan yara mata, da bautar da su da ake yi, da kuma hana su damar yin karatu mai zurfi a Arewacin Nijeriya.

Cikin ’yan watanni kaɗan, Sawaba ta samarwa kanta matsayi da suna a siyasar Nijeriya. A wani jawabi da ta yi a wani taron siyasa da aka yi a Zaria, inda ta mike a cikin ɗakin taron cike da maza, cikin kwarin gwiwa, ta gabatar da jawabin da mutanen wajen kowa ya ji shakkar buɗe baki ya ƙalubalance ta.

Gambo Sawaba ta ci gaba da daga darajarta ta hanyar bi gida-gida, inda ta ke tattaunawa da matan da ke da ra’ayin siyasa amma suna tsoron fitowa a dama da su, kawai saboda kasancewarsu mata, tana ƙarfafa musu gwiwa, da ba su shawarwari.

Dangin mijinta basa jin daɗin irin rawar da ta ke takawa a siyasance, saboda wannan dalilin uwar mijinta ta ɗauke ’yarta. Amma duk da haka ta ci gaba da jan hankulan matan Arewa a kan fitowa a dama da su a harkokin rayuwa.

A shekarar 1952, wata kotu ta ɗaure Gambo Sawaba a gidan yari na tsawon watanni uku, bisa zarginta da ake yi na cewa tana hurewa mata kunne, suna cire lilliɓi, kuma suna haɗa kafaɗa da kafaɗa da maza wajen gudanar da harkokin rayuwa. Shekara guda bayan ta gama wa’adin zaman gidan yarinta, hukumomi a Kano suka haramta mata zaman garin, inda aka haɗa ta da dogarai suka mayar da ita Zariya. Duk da haka ta ci gaba da harkokin siyasarta a garin na Zariya. An sake ɗaure ta a gidan yarin Kaduna, da kuma Jos.

A sakamakon azabtarwar da aka yi mata a gidan yari a 1957, sai da ta buƙaci a yi mata tiyata don a ceto rayuwarta daga larurar mafitsara da ta samu.

Gambo Sawaba ta rasu a watan Oktobar shekarar 2001. Ta rasu tana da shekaru 71 a duniya. Ta bar ’ya ɗaya.

Tarihi ba zai taɓa mantawa da Hajiya Gambo sawaba ba, saboda tasirin da ta ke da shi a Nijeriya, akwai katafaren Asibiti a garin Zariya mai suna Hajiya Gambo Sawaba General Hospital. Sannan akwai ɗakin kwanan ɗalibai mata a jami’ar Bayero da ke Kano, da aka sanyawa sunan Gambo Sawaba Hall.