Ba zan yi ritaya ba saboda na sha kashi – Anthony Joshua

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Anthony Joshua ya bayyana cewa ba shi da niyyar yin ritaya daga wasan dambe bayan da ya sha kaye a hannun Daniel Dubois ranar Asabar.

Dubois ya yi waje da Joshua a zagaye biyar a Wembley a daren Asabar.

Wannan shi ne karo na huɗu da Joshua ya sha kashi a fagen wasan.

Da aka tambaye shi ko zai sake fafatawa a shekara mai zuwa, Joshua ya ce a taron manema labarai “Wataƙila kuna tambaya ko har yanzu ina son ci gaba da wasan dambe, ba shakka ina son ci gaba da dambe.

Ya bayyana cewa shi dama wasa haka yake, wata rana ai nasara wata rana kuma ai rashin nasara. Saboda wannan rashin nasarar na zai sanya in daina wasan dambe ba.

Daga ƙarshe kuma ya ƙara da cewa dole ne mu ya yabawa abokin karawar shi, Daniel.

By ukarofi