Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya miƙa gaisuwar ‘Easter’ ga Kiristoci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Christopher Musa miƙa gaisuwar taya murna ga al’ummar Kirista bisa zagayowar bikin Easter musamman ga mambobin rundunar sojojin Nijeriya.

Daraktan yaɗa labarai na Hedikwatar Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau a wata sanarwa da ya fitar, Janar Musa ya jaddada muhimmancin lokacin bikin wajen sadaukarwa gami da nuna godiya ga nasarori acikin al’umma.

Ya ce, jami’an sojoji na amfani da damar wajen sadaukarwa a yayin gudanar da ayyukansu da tsare gaskiya ga ƙasa gami da tabbatar zaman lafiya acikin al’umma.

Ya kuma yaba wa ƙoƙarin jami’an bisa jajircewa wajen fuskantar haɗari a yayin daƙile ayyukan ta’addanci da wanzar da zaman lafiya.

Haka kuma ya yi addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu da jajanta wa waɗanda suka samu raunuka a yayin ayyukansu don ƙarfafa gwiwa ga iyalansu.

Har’ilayau, ya yi kira ga dakarun da su kasance masu sadaukarwa da yafiya da kuma haɗin kai a tsakanin su don ganin sun cimma nasara a yayin sauke nauyin da ke kansu.

By Babaji