Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta ‘Civilian Joint Task Force’ a Legas, Mista Kumar Sanda, ya tabbatar da cewa, ɗaruruwan mutane da ake zargin ‘yan Boko Haram ne aka kama a jihar Legas.
Kumar ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake jawabi a wajen wani bikin karramawa da aka gudanar a Legas, inda ya bayyana irin ƙoƙorin da rundunar CJTF ke yi na hana kutsen ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga da ke tserewa daga Arewa zuwa Legas.
A wajen taron da aka gudanar a otel ɗin Jiragen Sama da ke Legas, Kumar ya samu lambar yabo ta ƙungiyar Kare Haƙƙokin ɗan Adam ta Nijeriya Mafi Kyawun Tsaro a Legas.
A cewar kwamandan na CJTF, ana kama mutane akai-akai a wuraren shaƙatawa da ma’aikatu, wuraren kasuwanni, da sauran wuraren da aka san mutanen Arewa na taruwa idan sun isa Legas.
Ya tabbatar da ƙudurin CJTF na tabbatar da aikin gwamnatin jihar Legas na tabbatar da cewa jihar ba ta zama maɓoyar ‘yan tada ƙayar baya da ke tserewa a Arewa ba.
“Idan na ambaci adadin ‘yan Boko Haram da muka kama a jihar Legas, mutane ba za su yarda ba, amma mun kama ɗaruruwa,” inji Kumar.
Ya ƙara da cewa, “Boko Haram ba ta da wani yanki a jihar Legas, shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Legas a kullum yana tuntuɓar mu domin ganin mutane sun kwana cikin kwaciyar hankali.”
