Allah Ya yi wa Babban jami’in kamfanin jiragen sama na Max Air, Bashir Mangal, rauwa.
Sanarwar rasuwar ta fito ne ta hannun jami’in tuntuba kan sha’anin yaɗa labarai na kamfanin, inda ta nuna marigayin ya rasu ne da safiyar Juma’a.
Rahotanni sun nuna an yi jana’izar marigayin kamar yadda Musulunci ya tanadar a Katsina.
Bashir Mangal ƙani ne ga Dahiru Barau Mangal, mu’assasin kamfanin jiragen sama na Max Air, wanda jiragensa ke zirga-zirga a gida da ƙetare.
