Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, hukumar da ke tabbatar da ɗa’ar addinin Musulunci, ta kama wasu matasa 19 da suka halarci bikin auren jinsi.
Kakakin hukumar, Lawan Ibrahim ya bayyana haka a ranar Talata a Kano cewa matasan sun hallara ne domin shaida ɗaurin auren wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan liwaɗi ne Abba da Mujahid.
“An kama shi ne bayan da wani saurayi nagari ya tsegunta wa hukumar game da shirin auren jinsin.
“Jami’an mu da ke hedikwatar hukumar Hisbah, Sharaɗa Kano, sun isa wurin kafin a fara ɗaurin auren.
“A cikin waɗanda aka kama akwai mata 15 da maza huɗu,” inji Ibrahim.
“Abba da Mujahid sun tsere, nan take jami’an Hisbah suka isa wurin ɗaurin auren, amma mai shirya bikin, Salma Usman, ‘yar shekara 21, tana hannunmu.
“Waɗanda aka kama za a miƙa su ga ‘yan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace kamar yadda akasarin matan suka ce an gayyace su zuwa ɗaurin auren ne daga jihohin makwabta.
“Za mu kuma ƙara ƙaimi wajen ganin an kama Abba da Mujahid,” inji shi.
Ibrahim ya jaddada cewa hukumar ta ƙudiri aniyar kawar da duk wasu munanan ɗabi’u a jihar.
