Babban jigo a NNPP ya yaba wa Kwankwaso bisa kalamansa kan sanya dokar ta-ɓaci a Ribas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon Shugaban tsohuwar Jam’iyyar ANP kuma Darakta-Janar na majalisar yaƙin neman zaɓen Rabi’u Musa Kwankwaso a Arewa, Asiwaju Moshood Shittu, ya jinjina wa Kwankwaso bisa nuna dattako akan matsalar sanya dokar ta-ɓaci a Ribas, wanda Majalisar Dokoki a mataki na ƙasa ta amince da shi.

Ya ce, matakin da ɗaya daga cikin manyan ƙasar ya ɗauka ya nuna yadda ya ke da sanin ya kamata da kishi gami da ƙwarewa.

Ya kuma ce, Kwankwaso mutum ne wanda ba ya gaggawar tsoma baki akan wani abu don gamsar da mutane, saidai ya na la’akari ne da abinda dokar ƙasa ta tanada.

Shittu ya bayyana cewa, jagoran na jam’iyyar NNPP ya yi la’akari da hujjojin da ƴan majalisu suka kafa a ƙarƙashin na Shugaban Ƙasa, waɗanda dokar ƙasa ce ta bada damar yin hukuncin.

Ya ƙara da cewa, lallai Kwankwaso mutum ne mai hangen nesa, ya na mai kira ga sauran manyan ƙasa da su kwaikwayi irin nagartar tasa.

By Babaji