Babban Sakataren Ma’aikatar ƙasashen wajen ya musanta zargin cin zarafi

Spread the love

Babban Sakataren Ma’aikatar Ƙasashen waje ya musanta zargin cin zarafi da minista yayi masa a wata takarda da ministan ya aikewa shugabar ma’aikatan Najeriya ta hanyar lauyoyinsa.

Wasu waɗanda suka nemi a ɓoye sunayensu sun shaida cewa wannan tuhumar kawai faɗa ne tsakanin Ministan da Babban sakataren. Kuma sun shaidawa jaridar PR Nigeria cewa zargin cin zarafin ba zai yiyu ya zama gaskiya ba.

Wani cikin wanda ya nemi a sakaya sunan shi ya ce mataimakiyar Ministan ta nemi wasu alfarma ne wanda shi Babban sakataren ya hana wanda yake tunani shine sanadin yi masa wannan bita da ƙullin.

Kamar yadda Jaridar PR Nigeria ta rawaito cewa ta hangi wata takarda wadda take nuni da martanin lauyan Babban Sakataren in da suke musanta zargin.

By ukarofi