Daga NASIR S. GWANGWAZO
Daga dukkan alamu kotunan da ke sauraron taƙaddama kan gadon kagarar Masarautar Kano za su zauna a rana guda ne bayan da a jiya Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ta sanya ranar 13 ga Yuni, 2024, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci game da taƙaddama kan huruminta na sauraron shari’a kan masarautar.
Wannan rana da Babbar Kotun Tarayya ta sanya ya zo daidai da ranar Babbar Kotun Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ne a ranar 28 ga Mayu, 2024.Idan za a iya tunawa, taƙaddama kan shari’ar wanda ya cancanci hawa karagar Masarautar Kano ta zama abin ruɗani ne a lokacin da kotunan biyu suka bayar da umarni masu karo da juna.
Idan za a iya tunawa, Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis, 23 ga Mayu, 2024, Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya rattaɓa hannu kan sabuwar dokar da ta rushe masarautun Jihar Kano guda biyar (Kano, Bichi, Gaya, Qaraye da Rano) da naɗe-naɗensu, sannan kuma a washegari Juma’a, 24 ga ya dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, a matsayin Sarkin Kano na 16.To, amma jim kaɗan bayan ba shi sandar sarki sai Babbar Kotun Tarayyar ta bayar da umarnin dakatar da komai, ta kuma ɗage cigaba da sauraron ƙarar, wacce tuɓaɓɓen Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babban ɗan Agundi, ya shigar, har sai ta yanke hukuncin a ranar Litinin, 4 ga Yuni, 2024.A tsakar daren Asabar ne, Gwamna Abba ya jagoranci raka Sarki Sanusi II zuwa Fadar Masarautar Kano da ke ƙofar Kudu a tsakiyar Birnin Kano bayan da bayanai suka nuna cewa, jami’an tsaro na Gwamnatin Tarayya za su shigo da tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, zuwa fadar.A ranar Asabar ɗin kuwa, Alhaji Aminu Ado ya sauka a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar sojoji, ’yan sanda masu kaki da farin kaya da jami’an sibil defens suka yi ma sa rakiya zuwa fadar Gidan Nasarawa da ke wajen ganuwar Kano, inda ya sauka a can.A ranar Litinin ne Sarki Sanusi ya garzaya kotun Alƙali Amina, inda shi da masu naɗin sarki su ka amshi umarni na hana jami’an tsaro gallaza mu su, sannan kuma kotun ta bayar da umarni ga jami’an tsaron da su fitar da Alhaji Aminu Ado daga fadar Gidan Nasarawa tare da hana shi amsa sunan sarki.Washegari kuma sai wata Babbar Kotun Tarayya ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a S. Ambode ta bayar da umarni mai karo da wanda Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar bayan da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ƙara gabanta, don dakatar da jami’an tsaro daga haike ma sa.Ruɗanin ya kai ga har Alƙalin Alƙalan Nijeriya Olukayode Ariwoola ya yi sammacin Alƙalin Alƙalan Jihar Kano da na Babbar Kotun Tarayya kan batun. Tun daga lokacin aka yi cirko-cirko a na jiran yadda za ta kasance.Ranar Litinin ɗin da ta gabata Babbar Kotun Tarayya ba ta samu damar zamanta ba, saboda yajin aiki da ma’aikata suka tsunduma sakamakon taƙaddamar mafi ƙarancin albashi a Nijeriya.
Sai a jiya ne kotun ta samu zama bayan janye yajin aikin.A zaman na jiya, wanda Mai Shari’a Liman ya sauraro an yi taƙaddama ne kan hurumin Babbar Kotun Tarayya na sauraron shari’ar da ta shafi masarautu, inda lauyan ɓangaren Gwamnatin Jihar Kano, Mahmoud Abubakar Magaji (SAN), ya ƙalubalanta. Amma lauyan masu ƙara, Barista M. S. Waziri, ya yi togaciya da cewa, wannan shari’a ce ta neman ’yanci, wacce Aminu Babba ya ke nema, amma ba ta sarauta kaɗai ba.A yayin da ya ke bayar da umarni, Alƙali Liman ya sanya ranar 13 ga Yuni, 2024, don yanke hukunci kan cancantar hurumin kotun, inda ranar ta zo daidai da wacce Alƙali Amina ta sanya, don sauraron qarar da Sanusi II na shigar.Shin al’amarin dai ya yi kama da hadin baki ko haɗin kai? Lokaci ne zai tabbatar da hakan.
