Babu ɗan bindigar da zan ba wa sisin kwabo a matsayin fansa, inji Gwamnan Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jadda da matakinsa na ƙin goyon bayan dukkan wata tattaunawa da ‘yan bindigar da suke sace mazauna da haddasa firgici a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata hira da ‘yan jarida a ranar Litinin, inda ya ce bai wa ‘yan bindiga kuɗi abu ne da ke ƙara musu ƙarfi. Ya kuma ce, tattaunawar sulhu da aka yi da su a baya ba su bayar da kyawawan sakamako ba. “Kun san akwai wasu matakai masu tsauri da suka dace ka ɗauka a matsayinka na jagoran gida…kuma na yi bayanin cewa wannan ita ce matsayata, amma idan wani yana ganin saɓanin haka, zai iya zuwa ya je ya biya ya dawo da Yusuf da Amba gida,” inji Lawal yayin tunatar da garkuwa da ‘yan uwansa a shekerar 2025.

A lokacin har ta kai ga ‘yan bindigar sun rage matakin buƙatarsu zuwa neman a siyasa musu katin kiran waya na N150,000, wanda shi ma gwamnan ya ƙi amincewa da hakan. “Wani daga gidan ya yi haka saboda ni na riga na yanke shawarar ba zan bai wa ɗan bindiga ko sisin kwabo ba.” Wannan kalamai dai na zuwa ne yayin da ayyukan hare-hare da garkuwa daga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a Jihar Zamfara suka yi ƙamari a wannan shekara.

A watan Junairu ne aka halaka sojoji biyar da ɗan sanda a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka yi wa jami’an tsaro kwanton-ɓauna akan hanyar yankin Kwatarkwashi da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu. Sannan, a watan da ya biyo bayan hallau, an halaka mutane 30 da yin awon-gaba da wasu da dama yayin da wasu mahara suka farmaki ƙauyen Ɗan Ajiya da ke Ƙaramar Hukumar Anka. Haka kuma, an tabbatar da mutuwar mutane 11 a ƙauyen Ware da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe.

Bugu da ƙari, a watan Afrilu wasu ‘yan bindiga suka kai wa ƙauyen Kurfa na Ƙaramar Hukumar Bukkuyum farmaki, inda suka sace wani adadi na mazauna ‘yankin. Kwanaki kaɗan bayan haka dakarun tsaro suka ce sun halaka sama ‘yan bindiga 30 a wani arangama a Tsafe.

A watan Mayu ne kuma wani abin fashewa da aka dasa a hanyar Bagega zuwa Anka ya halaka mutum shida da raunata wasu, yayin da ‘yan bindiga suka yi wa matafiya kwanton-ɓauna akan hanyar Magami zuwa Ɗan-Sadau, inda aka halaka mutane da dama da yin awon-gaba da wasu.

Wannan fitina ta cigaba a watannin Yuni da Yuli, inda aka sace mazauna 39 yayin wani zaman sulhu a Maradun, sannan aka yi garkuwa da ɗalibai bakwai a Ƙauran Namoda. Har ila yau, a Yuli ne aka sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunguɗu bayan wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki a gidansa, inda suka halaka ‘yan sanda biyu, ɗan bijilante da wani farar hula.

Kazalika, a kwanan nan a watan Satumba dakarun tsaro suka ceto matafiya 41 da aka sace bayan motarsu ta kasuwa ta lalace akan hanyar Tsafe zuwa Funtua, lamarin da ke nuna matakin ƙalubalen tsaro a manyan titinan jihar. Saidai, gwamnan ya ce gwamnatinsa tana aiki tuƙuru wajen ganin ta inganta ayyukan jami’an tsaro akan matakan mayar da martanin hare-hare musamman a yankin Tsafe da aka fi samun matsalolin rashin tsaro.

By Babaji

Leave a Reply