Gwamnatin Katsina ta naɗa sabon kwamandan Hisbah a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta naɗa Muhammad Saifuddeen Yakubu Musa sabon babban kwamandan Hisbah a Jihar.

Naɗin ya biyo bayan murabus da Dr Aminu Usman (Abu Amar) tsohon shugaban hukumar ya yi.

Sabon kwamandan ɗa ne ga Sheikh Yakubu Musa Hassan sautus Sunnah shugaban ƙungiyar Izala a Jihar Katsina.

Mutane na ganin murabus da Dr Aminu Usman ya yi bai zo da mamaki ba domin tun a watanni baya ya bi bangaren Ibrahim Kabir Masari mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa.

Ibrahim Kabir Masari da Dikko Raɗɗa waɗanda duka ya’yan Jam’iyar APC a Jihar Katsina amma babu jituwa a tsakanin su.

By ukarofi

Leave a Reply