Duk ɗan majalisar da aka dakatar ya bada haƙuri za a maido shi bakin aiki – Kakakin majalisar Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Kakakin majalisar dokokin Jihar Zamfara, Rt. Hon. Bilyaminu Ismail Moriki ya ce duk wani ɗan majalisar da aka dakatar da ya zo ya ba da haƙuri kan laifin da ya aikata, za a maido shi domin ya ci gaba da gudanar da aikinsa na majalisa.

Hon. Moriki ya bayyana hakan ne a Gusau da yammacin yau, yayin da yake martani kan ficewar ƴan majalisa takwas da aka dakatar daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Ya ce ficewarsu daga jam’iyyar APC mai mulki ba ta shafi aikin majalisar dokokin jihar a ƙarƙashin jagorancinsa ba.

Ya ƙara da cewa majalisar na nan a tsaye, tana aiki, kuma tana da haɗin kai.

Ya bayyana cewa ƙofofin majalisar a buɗe suke don sulhu, inda ya kawo misali da wasu ƴan majalisa biyu da aka dakatar a baya amma suka ba da haƙuri kuma aka maido su nan take.

A cewarsa, dakatarwar ‘yan majalisar takwas da ta fara aiki a ranar 26 ga Fabrairu, 2024, ta samo asali ne daga aikata babban laifi, haɗa baki, raina Majalisa da kuma gudanar da zaman haramun, ba wai saboda siyasa ba.

Hon. Moriki ya bayyana ficewarsu ta baya bayan nan a matsayin wani yunƙuri na ƙirƙirar da yaudara cewa akwai rikici a majalisar.

Ya ce a ranar 13 ga Mayu, 2026, Majalisar ta amince da tsawaita dakatarwar su zuwa wani zaman majalisa na gaba saboda matsalolin ladabtarwa da ba a warware ba da kuma ƙarar laifi da ke gaban kotu da ta shafi fasa gida, kutsawa da ƙarfi da kuma lalata dukiyar gwamnati a harabar majalisar.

Ya sake jaddada cewa sauya sheƙa ta jam’iyyar siyasa ba ta soke batutuwan ladabtarwa na majalisa ko kuma shari’o’in da ke gaban kotu ba.

Kakakin ya ƙara jaddada aniyar majalisar na kare mutuncin majalisa da kuma goyon bayanta ga manufofin gwamnatin jihar.

Ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da jita jitar da ke cewa majalisar na cikin rikici, yana mai cewa an gudanar da zaman majalisa a ranar Talatar da ta gabata da kuma yau Litinin, 5 ga Oktoba, 2026, kuma majalisar za ta sake komawa gobe.

By ukarofi

Leave a Reply