Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta ce ‘Yarjejeniyar Samoa’ da gwamnatin ƙasar ta sa hannu a kai ba ta da wata alaƙa da auren jinsi da ake cece-kuce a kai.
Shugaban NBA, Yakubu Maikyau, ya ce ƙungiyar na da hannu wajen sanya hannu kan yarjejeniyar Samoa kuma babu wani ɓangare na yarjejeniyar da ke da alaƙa da ’yan luwaɗi da maɗigo, ko auren jinsi (LGBTƘ).
Shugaban na NBA ya ce ƙungiyar ta lura da ce-ce-ku-cen da ake a Nijeriya kan rattaɓa hannu da ƙasar ta yi kan yarjejeniyar Samoa wanda ake zargin an sharɗanta mata amincewa da karewa ko yarda da haƙƙoƙin LGBTƘ, don samun rancen kuɗi Dala biliyan 150.
Maikyau, a cikin wata sanarwa a safiyar Talata, ya ce, “Babu wani tanadi a Yarjejeniyar Samoa da ke buƙatar Nijeriya ta amince da ’yan luwaɗi ko auren jinsi a matsayin sharaɗin samun rancen Dalar biliyan 150.
“Maimakon haka, yarjejeniyar ta amince ta kasance a ƙarƙashin dokokin ƙasar da kuma ikon ƙasar na cin gashin kai.
“Wato Yarjejeniyar Samoa ta amince, misali, da dokar haramcin auren jinsi ta Nijeriya ta 2023 da kuma ikon kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999.”
Ya ƙara da cewa da akwai wani tanadin yarjejeniyar da ya saɓa wa dokokin Nijeriya da ƙungiyar ta shawarci gwamnati kada ta sanya hannu.
Da yake shawartar ’yan Nijeriya da su kasance masu taka-tsan-tsan, Shugaban na NBA ya ce ƙungiyar na sa ido kan ayyukan gwamnati tare da yin tsayuwar daka wajen kare al’umma a kowane lokaci.
