Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja ta aike da mutumin da aka kama da yunƙurin kashe kansa zuwa Cibiyar Kula da Masu Lalurar Ƙwaƙwalwa (SDS) domin tantance lafiyar ƙwaƙwalwasa.
Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ne ‘yan sanda suka kama Shu’aibu Yushau da laifin hawa tsaunin gidan rediyon ASO da ke Katampe, Abuja, da yunƙurin kashe kansa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya cewa, za a ɗauki mataki kan wanda ake zargin idan har aka ga lafiyar ƙwaƙwalwarsa ƙalau.
Ya ce, “Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, a yau, 9 ga watan Yuli, 2024, ta aika da Shuaibu Alhaji Yushau zuwa SDS domin auna lafiyar ƙwaƙwalwsa da sanin ya kamata, biyo bayan matakin da ya ɗauka na damun jama’a a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli. , 2024, ta hanyar hawa babban layin sadarwa na ASO Radio dake Katampe, Abuja, da yunƙurin kashe kansa.
“Wanda ake zargin, idan aka same shi da lafiyar kwakwalwa bayan an kammala gwajib, za a gurfanar da shi a gaban kotu bisa laifin yunƙurin kashe kansa, da hargitsa zaman lafiyar jama’a, da kuma tada zaune tsaye da ya saɓawa sashe na 231, 111, da 114 na dokar aikata laifuka.
“Kwamishanan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, CP Benneth C. Igweh ya buƙaci mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda, yayin da suke ƙoƙarin a ji muryoyinsu, domin ba za a yi tilasta ’yan sanda barin doka da oda ba,” inji ta.
