Dogarin Tinubu ya zama sabon Sarkin Ilemona a Jihar Kwara

Spread the love


Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An naɗa Laftanar Kanal Nurudeen Yusuf, dogarin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a matsayin sabon Sarkin Garin Ilemona da ke Jihar Kwara.
Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzu Yusuf na kan karagar mulki ne a matsayin ‘Adele’ (Shugaba) domin duba al’amuran garin har sai ya yi ritaya daga aikin Soja.
Yusuf dai ɗa ne ga marigayi sarki Oba Yusuf Omokanye Oyekanmi, Elemona na Ilemona a ƙaramar hukumar Oyun a Jihar Kwara.
Bayan ya kammala karatunsa na digiri a fannin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa daga kwalejin fasaha ta Offa a shekarar 2000, Yusuf ya shiga makarantar horar da sojoji ta Nijeriya da ke Kaduna, inda ya kammala digirinsa na farko a fannin Injiniyanci.
Tsakanin 2004 zuwa 2005, ya halarci makarantar Royal Military Academy Sandhurst (RMAS), a Birtaniya.
A shekarar 2006, ya halarci makarantar leƙen asiri ta sojojin Nijeriya da ke Legas inda aka horar da shi a fannin leƙen asiri da darussa da suka shafi tsaro kamar yadda tsarin horar da sojojin Nijeriya ya tanadar.
Halartar wani kwas na Young Officer’s Course Infantry, NASI, wani kwas a Kaduna a 2007 ya ba shi ilimin aikin soja kan amfani da nau’ikan makaman da ake amfani da su a cikin rundunonin sojoji da kuma ayyuka na musamman.
A shekara ta 2008, Yusuf ya kammala kwasa-kwasan jami’an leƙen asiri da kuma kwasa-kwasan binciken tsaro don inganta kwarewarsa a matsayinsa na soja.
A tsakanin shekarar 2009 zuwa 2018, jami’in mai yarukan harsuna da dama, wanda ya kware a harsunan Yarbanci da Hausa da Ingilishi da Faransanci, ya samu horon soji da dama a ƙasashen Mali da Pakistan da Chana da Isra’ila da kuma Birtaniya.
Horon ya haɗa da Koyarwar Hafsoshin Soja (Mali); Ƙwararrun Ma’aikata (Chana); Jami’ai Adɓanced Intelligence Course, SMI, (Pakistan) Adɓanced Command and Staff Course (Shriɓenham UK).
Yayin da yake samun horon aikin soji, Yusuf ya samu digirin digirgir a fannin tsaro daga Kwalejin Kings da ke Landan a shekarar 2018, sannan ya samu shaidar kammala karatun digiri na biyu a fannin nazarin zaman lafiya da warware rikice-rikice daga Jami’ar Nijeriya ta NOUN.
A kwanakin baya ne Yusuf ya kammala wani kwas ɗin soja da aka tsara domin kwamandoji a barikin sojoji na Jaji da ke Kaduna, kafin naɗa shi dogari ga zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar

By ukarofi