Babu biyan kuɗi ga duba baƙin gilashin mota, inji ƴan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda ta yi gargaɗin cewa babu biyan kuɗi game da bada damar amfani da baƙin gilashin ga masu ababan hawa.

A wata sanarwa, rundunar ta hana karɓar kuɗi daga masu motoci akan amfani da irin gilashin.

Ta ce, babu karin kuɗi da ake buƙata a yayin duba waɗanda lamarin ya shafa ko kuma neman izinin amfani da shi.

Ta kuma yi kira ga al’umma da su gaggauta ruwaito mata duk inda aka samu ana karɓar kuɗi akan batun, ta na mai cewa ta yi hakan ne don tabbatar da gaskiya da adalci da kuma tsare amanar al’umma.

By Babaji