Sammaci: Majalisun dokokin Benuwai da Zamfara sun maka Majalisar Wakilai a kotu

Spread the love

daga USMAN KAROFI

Majalisun dokoki na jihohin Benuwai da Zamfara sun bayyana cewa ba za su amsa gayyatar da kwamitin koke na majalisar wakilai ta tarayya ya aika musu ba. Sun ce wannan mataki ya saɓawa kundin tsarin mulki kuma yana nuni da ƙoƙarin kwace ikon majalisun jihohi.

An gayyaci gwamnonin jihohin biyu, Hyacinth Alia na Benuwai da Dauda Lawal na Zamfara tare da shugabannin majalisunsu da su bayyana a gaban kwamitin a ranar Alhamis, 8 ga Maris, 2025.

Majalisar Dokoki ta jihar Benuwai ta yanke shawarar cewa Shugabanta, Hyacinth Dajoh, ba zai halarci wannan gayyata ba, tana mai cewa Majalisar Tarayya ba ta da hurumin da ya bata ikon kiran majalisar jihar domin tambayoyi. Shugaban masu rinjaye a majalisar, Saater Tiseer, ya ce sashe na 101 na kundin tsarin mulki ya bai wa majalisar ikon tsara yadda take gudanar da aikinta ba tare da katsalandan daga waje ba.

Wasu ‘yan majalisar kamar Bemdoo Ipusu, Michael Audu da Peter Uche, sun goyi bayan matsayar majalisar. Ipusu ya nemi a kai ƙara kotu domin hana Majalisar Tarayya ci gaba da shirin ƙwace aikinta, tare da zargin ƙungiyar “Guardians of Democracy” da yaudarar Majalisar Wakilai. A sakamakon haka, an shigar da ƙara a babban kotun tarayya da ke Makurdi domin neman dakatar da Majalisar Wakilai daga ci gaba da shirin.

A nata ɓangaren, Majalisar Jihar Zamfara ta ce gwamna Dauda Lawal ba zai bayyana a gaban kwamitin Majalisar Wakilai ba. Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Kabiru Ɗangulbi, ya bayyana gayyatar a matsayin “marar tushe kuma haramtacciya” bisa ga dokar ƙasa. Sai dai, ya ce Zamfara ba za ta ɗauki matakin kotu ba, yana mai fatan Majalisar Tarayya za ta gane kurenta.

By ukarofi