Inter Milan ta kai wasan ƙarshe a Champions League bayan doke Barcelona

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Milan dake ƙasar Italiya, ta doke Barcelona da jimillar ci 7 da 6 a wasan dab da na ƙarshe na gasar zakarun Nahiyar Turai, Champions League.

A wasan zagaye na biyu ne ƙungiyar ta yi nasara akan Barcelona da ci 4-3 bayan wasan ya kai su zuwa zangon ƙarin lokaci na biyu.

A karawar farko a gidan Barcelona an tashi ne kunnen doki a tsakanin kungiyoyin bayan da suka yi 3-3 a filin wasa na Nou Camp.

A yanzu dai Inter za ta fafata da ɗaya daga cikin wadda ta yi nasar a wasan PSG da Arsenal da za a yi a daren yau Laraba.

A ranar 31 ga watan Mayu, 2025 ne za a buga wasan ƙarshen a Filin Allianze Arena da ke birnin Munich a ƙasar Jamus.

By Babaji