
Daga BELLO A. BABAJI
An zargi wata sabuwar amarya mai suna Saudat Jibrin Adam da kisan angonta mai suna Salisu Idris Ibrahim, kwanaki tara da ɗaura aurensu a yankin Farawa dake Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.
Lamarin ya auku ne a daren ranar Talata wanda ya yi sanadin jafe al’ummar yankin cikin firgici.
Shaidu sun bayyana cewa, matar ta yaudari mijin ne ta hanyar faɗa masa cewa ya rufe idonsa domin ta yi masa ba-zata, inda daga nan sai ta yi amfani da wuƙar da ta ɓoye wajen yanke masa maƙogwaro.
Wani maƙocinsu da ya shaidi lamarin mai suna Dini Mada, ya faɗa wa manema labarai cewa, gabannin mutuwarsa, Salisu ya gano cewa matarsa ce ta faramke shi a lokacin da ya ke gararin mutuwa a asibiti.
Ya ce, “Na tambaye shi wa ya maka haka. Ya ce, Dini matata ce ta yanka ni da wuƙa a falo. Ce mun ta yi na rufe idona za ta mun ba-zata, saidai ban san ta ɓoye wuƙanta a wani waje ba. Ta yanke ni a wuya”, inji Dini a hirarsa da mamacin gabannin mutuwarsa a asibiti.
Daga bisani, ƴan sanda a yayin bincike suka gano matar a wani ɗaki da ta kulle kanta aciki, inda aka same ta a lokacin da ta ke yin waya.
Bugu da ƙari, Dini ya ce wani abokin mamacin na kusa ya ce ma’auratan suna da wata matsala a tsakaninsu da ba a kai ga warware ta ba, wadda makusantan mijin ne kaɗai suka san da ita.
Ya ƙara da cewa, ta kai su ga amaryar ba ta dafa masu abinci, inda a wasu lokutan sai dai ya sayo dafaffen abinci ya kawo musu.
Rundunar ƴan sandan jihar ta ce, za ta yi bincike game lamarin, kana daga bisani ta bayyana wa al’umma, kamar yadda Kakakinta SP Abdullahi Kiyawa ya shaida wa jaridar WikkiTimes.
