Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya mayar da martani game da wani allon sanarwa da aka kafa a birnin Katsina, lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo ziyara a jihar.
Allon na nuna cewa al’ummar jihar Katsina ba su da ƙorafi game da mulkin shugaba Tinubu, sai dai lamarin ya janyo cece kuce daga ciki da wajen Jihar Katsina.
A cewar gwamna Raɗɗa wasu ne suka kafa allon “Katsina ba ƙorafi” madadin a sanar da shi sai mutane suka riƙa yaɗa hoton a kafafen sadarwa na zamani.
Gwamnan ya cigaba da cewa, sun gabatar ma shugaba Tinubu ƙwararan ƙorafe-ƙorafe har guda uku da ke buƙatar a magance wa jihar wanda suka haɗa da matsalar tsaro, kammala aikin jawo wuta mai amfani da hasken rana, da kuma faɗaɗa filin sauka da tashin jirage na Umaru Musa Yar’adua da ke jihar ta Katsina.
Daga ƙarshe gwamnan ya ja hankalin masu suka da su riƙa tantance labarin da suka gani a kafafen sada zumunta domin tabbatar da asalin labari, kafin sukar wanda baya da masaniya a kai.
