
Babu wata al’ada, matsin tattalin arziƙi, ko zamantakewa da zai iya tabbatar da wahalar da miliyoyin mata da ƴan mata ke sha. Aikinmu shi ne mu kalubalanci waɗannan labarai masu cutarwa.
Rashin daidaito tsakanin jinsi da cin zarafin mata na daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar ci-gaba mai ɗorewa, ba kawai a Nijeriya ba, har ma a duniya baki ɗaya.
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, a duniya kimanin mata miliyan 736, kusan kaso ɗaya daga cikin uku na fuskanci cin zarafi ta jiki ko ta hanyar jima’i, cin zarafi na jima’i, ko duka biyu aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu, wanda ke wakiltar kashi 30 cikin 100 na mata masu shekaru 15 zuwa sama, wannan adadi bai haɗa da cin zarafin ta hanyar jima’i ba.
Cin zarafin mata da ƴan mata take hakkin bil’adama ne. Ya na lalata ƙa’idodin daidaito, mutunci, da mutuntawa. Wannan tashin hankali yana ɗaukar nau’i-nau’i da yawa na jiki, na rai, jima’i, da kuma tattalin arziƙi; kuma yana faruwa a kowane yanki na duniya, ciki har da Nijeriya.
Daga cin zarafi na ƙud-da-ƙud zuwa ga al’adun gargajiya masu cutarwa irin su kaciyar mata, fataucin mutane, cin zarafi, yanayin cin zarafi da ya danganci jinsi dake nuna tushen rashin daidaito tsakanin al’umma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa matan da suka fuskanci tashin hankali sun fi fama da damuwa, da kuma matsalolin damuwa tare da mummunar sakamako na tsawon lokaci.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da yanayin cin zarafin mata a duniya: “Aƙalla mata 51,100 a 2023, dake fuskantar cin zarafin jinsi suka rasa rayukansu a hali na rashin tausayi, kisan su daga abokan tarayya da danginsu. Ma’ana ana kashe mace ɗaya a kowane minti 10.”
A Nijeriya, ana samun tashe-tashen hankula da munanan ayyuka ga mata da ƴan mata a kowace rana, kuma galibi ba a kai rahotonsu ba. Binciken Kiwon Lafiyar Jama’a da Lafiya ta Nijeriya a shekarar 2018 ya nuna cewa kashi 9 cikin 100 na mata masu shekaru 15 zuwa 49 sun fuskanci cin zarafi aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu kuma kashi 31 sun fuskanci cin zarafi. Ƙuntatawa da abubuwan da ke haifar da cutarwar sun ta’azzara ne ga cin zarafi na tushen jinsi (GBV) a cikin kasa.
Ɗaya daga cikin tsare-tsare na duniya da ke bada haske kan batun cin zarafin mata shi ne kwanaki 16 na fafutukar yaƙi da cin zarafin mata da za a fara a ranar 25 ga Nuwamba, ranar yaƙi da cin zarafin mata ta duniya, kuma za a kare a ranar 10 ga Disamba, Ranar ‘Yancin ɗan’Adam. Wannan lokaci ya kasance wani muhimmin dandali na wayar da kan jama’a, da ɗaukar matakai, da neman kawo ƙarshen duk wani nau’i na cin zarafin mata da ƴan mata.
A cikin waɗannan kwanaki 16 na faɗakarwa, bari mu yi tunani ba kawai a kan labarun ciwo ba, amma kuma mu yi murna da ƙarfi, juriya, da jaruntaka na mata da ƴan mata a Nijeriya da sauran duniya.
Mu mutunta muryoyinsu kuma mu himmatu ga makomar da ba ta da tashin hankali. Lokaci ne da za mu yi tunani a kan ci-gabanmu kuma mu yarda da aikin da ke gabanmu.
“Babu uzuri. Haɗa kai domin kawo karshen cin zarafin mata” shi ne taken bana, kuma a cewar Sakatare-Janar na MƊD, Antonio Guterres, yana nufin tsayawa tare da masu fafutuka a duniya da ke kira da a kawo sauyi da kuma tallafawa waɗanda suka tsira daga tashin hankali. Kira ne mai ƙarfi ga aiki. Yana tabbatar da alhakinmu na gama gari don tabbatar da cewa babu wata mace, ko yarinya da ke fuskantar tashin hankali a gidajensu, al’ummominsu, ko wuraren aiki. Tashin hankali ta kowacce hanya.
Yana da matuƙar muhimmanci mu haɗa kai a ƙoƙarinmu na kawar da tashin hankali a kowane irin yanayi.
Wajibi ne mu haɗa kai da gwamnatoci, ƙungiyoyin fararen hula, ƙungiyoyin Ƙasa-da-ƙasa, da kamfanoni masu zaman kansu don magance tushen tashin hankali.
Mu na buƙatar mu fuskanci halaye masu cutarwa, ra’ayoyi, da ƙa’idoji na nuna wariya waɗanda ke dawwamar da al’adar tashin hankali. Yana da mahimmanci a karya shiru da tabbatar da cewa waɗanda suka tsira sun samu tallafi da kariya da suke buƙata don sake gina rayuwarsu.
Babu hujjar cin zarafin mata. Babu wata al’ada, matsin tattalin arziƙi, ko zamantakewa da zai iya tabbatar da wahalar da miliyoyin mata da ƴan mata ke sha. Aikinmu shi ne mu ƙalubalanci waɗannan labarai masu cutarwa. Haƙƙi ne na haɗin-gwiwa don tabbatar da cewa kowacce mace da yarinya za su rayu ba tare da tsoron tashin hankali da wariya ba. Dole ne mu samar da yanayi mafi aminci inda mata da ƴan mata za su iya samun ilimi, aiki, sabis na kiwon lafiya, da gudanar da rayuwa mai gamsarwa ba tare da tsoro ba.
Yayin da Nijeriya ta bi sahun sauran ƙasashen duniya wajen bikin kwanaki 16 na fafutukar yaƙi da cin zarafin mata da maza, na tsaya tare da al’ummar duniya wajen bayyana gaskiya cikin gaggawa: Babu wani uzuri ga masu cin zarafin mata da ƴan mata.
Wannan ba batun muhawara ba ne; kira ne da a ɗauki matakin gaggawa. Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ta tsaya tsayin daka wajen yaki da tashe-tashen hankula a kowane ɓangare. Mun jajirce a kan ƙudirinmu na tallafa wa gwamnatin Nijeriya da duk masu-ruwa-da-tsaki don kawo ƙarshen cin zarafin mata.
Ayyukanmu a Nijeriya sun fi mayar da hankali ne kan ƙarfafa tsarin shari’a, inganta samun adalci, da kuma samar da wayar da kan jama’a don canza tunani da halaye.
Amma ba za mu iya yin wannan kaɗai ba. Muna buƙatar tallafi daga kowa: shugabannin al’umma, cibiyoyin addinai, malamai, da ɗaiɗaikun mutane. Yana da mahimmanci a haɗa maza da yara maza a matsayin abokan tarayya a cikin wannan yaƙin, ƙarfafa musu su yi magana game da tashin hankali, ƙalubalantar ƙa’idodin jinsi masu cutarwa, da haɓaka mutuntawa da daidaito a gidajensu da al’ummominsu.
Dole ne kuma mu tabbatar da cewa waɗanda suka tsira daga tashin hankali sun samu damar yin amfani da ayyuka da albarkatun da suke buƙata don warkarwa da sake gina rayuwarsu. Wannan ya haɗa da kiwon lafiya, taimakon doka, da ayyukan yau da kullum na shawarwari. Yana da muhimmanci a ƙirƙiri wurare inda waɗanda suka tsira za su iya ba da labarinsu ba tare da tsoron ramawa ba da kuma inda aka kiyaye mutuncinsu.
Tare za mu iya buɗe cikakkiyar damar kowane dan Nijeriya kuma mu gina makoma inda daidaiton jinsi ba buri ba ne kawai amma a tabbatar da gaskiya.
Babu hujjar cin zarafin mata, tare, za mu iya maganain nuna bambanci, tare, za mu iya gina duniya da ta kuɓuta daga tashin hankali da wariya. Duniyar da mata za su iya rayuwa tare da mutunci da girmamawa.
