Babu wani yunƙuri da ake na tsige ni —  Akpabio

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio, ya ce rahotannin da ke nuni da cewa hukumar tsaro ta DSS ta karɓe ikon majalisar don hana wani shirin tsige shi ba gaskiya ba ne.

Rahotannin sun ce jami’an tsaro sun mamaye dukkan ƙofofin shiga ginin majalisar a ranar Laraba.

TheCable ta rawaito cewa da ya ke magana a zauren majalisar dattijai, Akpabio ya ƙaryata rahotannin a matsayin “labaran ƙanzon kurege”.

Shugaban na majalisar dattijai cikin raha ya ce masu yaɗa wannan labari na iya neman samun kuɗaɗen shiga daga yawan yaɗuwar labarin a shafukansu na yanar gizo.

“Sun ce DSS ta mamaye majalisar dokoki don yiwuwar hana tsige shugabannin majalisa,” in ji shi.

“Babu iyaka ga kafofin sada zumunta, muna zaune a nan muna aikinmu cikin kwanciyar hankali ba tare da damuwa da fitinar da ake yi ba.

“Wane kwamitin za mu tura wannan batun? Sai aka bushe da dariya a majalisar.

By ukarofi