Daga JOHN D. WADA a Lafiya
A yayin da duniya baki ɗaya suke gudanar da bukukuwan bikin ranar masu taɓin hankali wato World Mental Health Day a Turance na 2024, Dr. Paul Agbo wanda shi ne shugaban sashin kula da masu taɓin hankalin na Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya dake Lafiya babban birnin jihar Nasarawa ya buƙaci ƙarin albashi wa ma’aikata a duka matakai don ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya yi kiran ne jim kaɗan bayan wani zagaye na musamman don tunawa da ranar ta masu taɓin hankalin wanda sashin ta shirya ta gudanar a Lafiya.
Ya bayyana cewa muddin ƙwaƙwalwar ma’aikata ba Lafiya ba za su iya yin aiki yadda ya dace ba.
Dokta Paul Agbo ya cigaba da bayyana cewa, ”idan mutane suna bakin ciki basa murna ko samun wadata ko yabo to fa babu yadda za su aiwatar da aikin a zo a gani. Shi ya sa muka yanke shawarar gudanar da bikin a yau don mu wayar da kawunan al’umma baki ɗaya. Wannan a taƙaice shine maƙasudin gangamin.
”Bincike ya nuna cewa abubuwa dake jawo taɓin hankali suna da yawa kamar wasu ƙalubalen rayuwa da sauran su ba hauka irin da aka saba gani kaɗai ba,” inji shi.
Dakta Paul Agbo ya kuma bayyana cewa ya kamata a riƙa yi bikin a kowace ranar 10 ga watan 10 a shekara ne amma bana sun yanke shawarar gudanar da shine a ranakun 15 da 16 na watan Oktoba na shekara da ake ciki 2024 daki-daki inda ya kuma sanar cewa taken bikin na bana shine ‘Tabin hankali da wajen aiki’.
