Badaƙalar haramta Tiwita a Nijeriya: Sulhu shi ne mafita – Ƙasashen Turai

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatocin Birtaniya (UK), Kanada, Jamhuriyar Ireland, Norway da na Tarayyar Turai (EU) sun yi kira da a tattauna don warware matsalar da ke tsakanin Nijeriya da Tiwita

A wani bayanin haɗin gwiwa da suka fitar a Asabar da ta gabata a Abuja aka kuma raba wa manema labarai, ƙasashen sun ce suna goyon bayan ‘yancin faɗin albarkacin baki da kuma damar samun bayanai a matsayin ginshiƙin dimukuraɗiyyar Nijeriya kamar dai yadda lamarin yake a sauran ƙasashen duniya, wannan ‘yancin kuwa ya shafi amfani da intanet da kishiyar haka.

A cewarsu, “Ɗaukar matakin dakatar da wani al’amari ba shi ne mafita ba. Wannan mataki ka iya illa ga damar samun bayanai da harkokin kasuwanci a daidai lokacin da Nijeriya ta fi buƙatar amfani zaman tattaunawa da kuma damar bayyana ra’ayoyi.”

Sun ce sun lura da cewa hakan na da muhimmanci musamman idan aka yi la’akari da batun annobar korona.

Haka nan, sun ce hanyar ci gaba da inganta sha’anin tsaron Nijeriya ta ta’allaƙa ne ga mara wa ƙoƙarin ‘yan ƙasa da yawan sadarwa don samun haɗin kai, zaman lafiya da kuma bunƙasa.

A cewar ƙasashen, “A matsayinmu na abokan mu’amalar Nijeriya a shirye muke da mu tallafa mata wajen cimma waɗannan buƙatu.”

Idan dai za a iya tunawa a baya Manhaja ta ruwaito yadda Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Tiwita da harkar microblogging da sohiyal netiwokin a faɗin Nijeriya har sai abin da Allah ya yi.

Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bada sanarwar dakatarwar a Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata.