Kudancin Nijeriya zai daina ganin albasa daga wannan Litinin har sai an biya mana buƙatunmu – Ƙungiya

Daga UMAR M. GOMBE

Ƙungiyar Manoman da ‘Yan Kasuwar Albasa ta Nijeriya (OPMAN), ta ce za ta dakatar da kai albasa ya zuwa Kudancin ƙasa daga wannan Litinin har sai gwamnatin trayya da na jihohi sun biya mata buƙatunta.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Malam Aliyu Isa ne ya bayyana haka a Sakkwato a Asabar da ta gabata sa’ilin da yake yi wa manema labarai bayanin matsayinsu.

Daga cikin jerin buƙatun da ƙungiyar ke neman a biya mata su har da biyan cikakken diyya ga mamabobinta waɗanda rikicin addini da na ƙabilanci ya shafa a yankin Kudu.

Haka nan, ta buƙaci a tabbatar da doka da oda a jihohin da ake fama da rikice-rikice tare da gudanar da bincike mai zurfi domin bankaɗo waɗanda ke da hannu a kai wa mamnobinta hare-hare.

Ƙungiyar ta buƙaci ‘yan yankunan da lamarin ya shafa da su zamo masu mutunta haƙƙoƙin ‘yan Arewa mazauna jihohinsu.

A cewar Malam Isa mambobinsu sun tafka hasarar albasa da sauran dukiyoyinsu da ya kai naira biliyan N4.5 sakamakon hare-haren da aka kai musu a yankin Kudu.

Ya ce a lokacin rikicin Aba a jihar Abia, sun rasa mambobi uku tare da ƙona musu motoci da dama da kuma buhun albasa 10,000 da sauransu.

Ya ci gaba da cewa, yayin rikicin Sasha na jihar Oyo kuwa, kimanin mutum 27 ne suka rasu, an ƙona motoci da dama haɗa da buhun albasa 5,600, kana aka sace albasa da kuɗinta ya kai naira milyan N13 a jihar Imo.

Ya ƙarasa da cewa, “Bayan tattaunawa da Shugabanin ƙungiyar suka yi da kuma duba da gazawar da gwamnati ta yi wajen share mana hawaye mun yanke cewa za mu dakatar da kai albasa zuwa yankin Kudu baki ɗayansa daga ranar Litinin, 7 ga Yuni, 2021 har sai an biya mana duka buƙatunmu.”