Bahaushe mai tashi mu je

Spread the love

Da farko ina amfani da wannan kalma ce domin mu faɗakar da juna ta fuskar gano illar ma su ɗabi’a ta tashi mu je. kalmar tashi mu je daga jin ta za a fahimci ta tattaro yaudara da ƙarya tare da ba ta lokaci ga wanda duk a kai ma hakan. Jama’a har kullum mu riƙa yi wa kawunan mu awo na adalci a madadin ga matsala a tattare da mu a gefe mu nai ma wasu kallon su ne ma su aikata laifuka.

Misalin tashi mu je, mutum ne ka na zaman ka zai zo ko kuma ya kirawo ka a waya yai ma ka albishir da wata samayya a zahiri wanda a qarshe idan tafiya tai nisa ka rasa inda wancen alƙawarin ya ke. A tsarin Musulumci an hane mu da yin karya. Haka an hane mu da yaudara wanda duka munanan ɗabi’u ne da su ka zamo jiki ga wasu a yau.

Kar ka yi ma mutum alƙawari na karya kawai domin ka burge shi. A kullum mu zamo masu gaskiya tun daga zuci da a aikace. Mu guji yin karya ko neman suna kawai domin mu burge. Gaski ita ke tabbata.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa.07066434519/08080140820.

By Editor