Ana zargin almundahana a rabon kayan tallafin Kebbi 

*An dakatar da rabon tallafin Argungu

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Gwamnan Jihar Kebbi, Malam Nasir Idris wanda shine Ƙauran Gwandu, ya ƙaddamar da rabon kayan tallafi a Ƙaramar Hukumar Maiyama, don rage raɗaɗin matsin tattalin arziki ga al’ummar jihar, inda kuma daga nan ya umarci kowacce ƙaramar hukumar mulki ta je ta raba a yankinta. Sai dai ba a nan gizo ke saƙa ba, saboda rabon kayan ya samu tarnaƙi yayin da a ke zargin tafka almundahana a waɗansu ƙananan hukumomi.

Wata mata da ba ta so a bayyana sunanta ba ta ce, ta cike fom kuma da hotonta, amma daga baya aka ce ba ta cikin jerin sunayen da za a bai wa tallafin.

Ta qara da cewa, su na ji ana kiran sunayen waɗansu mutane ’yan salain ƙananan hukumomin Birnin Kebbi da Jega a maimakon Argungu, waɗanda ba ’yan asalin Argungu ɗin ba ne, saboda haka ta ce ba za su yarda wannan ba. Mutanen garin na Argungu sun zargi ana neman a ci da haƙƙinsu.

A ƙaramar hukumar mulki ta Argungu an karɓo kayan da ya kamata a bai wa mutane 1,600, amma waɗanda aka zo da sunayensu mutane 500 ne, wanda hakan ya haifar da hayaniya a wajen rabon kayan. 

Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Aliyu Sani Gulma, ya bayyana wa manema labarai cewa, gaskiya ne an karɓo kayan mutane 1,600, amma saboda dalili na tsaro ba za iya fitar da kayan duka ba, don kada a wawashe, amma sai dai aka kira mutane 500 bayan an sallame su, sai a sake kiran waɗansu.

Sai dai Shugaban Ƙaramar Hukumar Argungu, Honarabul Salihu Ahmed KC, bayan samun waɗansu rahotanni da ke zargin tafka almundahana, ya dakatar da rabon kayan har sai an yi abinda ya kamata.

Wakilin Blueprint Manhaja ya nemi jin ta bakin Alhaji Aliyu Abddullahi, Shugaban Kwamitin Rabon Tallafin a Ƙaramar Hukumar Argungu, sai dai bai ɗauki waya ba kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai kira ko ya amsa ba.

Amma daga dukkan alamu ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, domin rahotanni daga ƙananan hukumomin Maiyama da Augie sun bayyana an yi rabon tallafin kuma ba tare da wani ƙorafi ba, sai dai abinda ba a rasa ba, saboda an yi rabon cikin tsarin raba kayan a matakin mazaɓu.